Jump to content

Maryam Abubakar (Jan kunne)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Maryam Jan Kunne ta kasance tsohuwar jaruma ce a cikin masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ta Dade tana fim daga baya tai aure.[1]

Takaitaccen Tarihin Ta

[gyara sashe | gyara masomin]

Cikakken sunan ta shine Maryam Abubakar Amma anfi sanin ta da maryam Jan Kunne a masana'antar. Haifaffiyar jihar Kano ce Kuma ta girma a jihar Kano. Tana kuma ɗaya daga cikin manyan jarumai da sukai tashe suka daukaka a masana'antar, ta kuma ɗaukaka ne sanadiyyar jarumi sani danja. Taking fina finai sama da Dari a masana'antar tafi fitowa a fim tare da jarumi sani danja da Kuma ubale Wanke Wanke. Fim din daya daukaka ta shine fim din "Jan Kunne" dalilin da ake mata lakabi dashi kenan.[2]

Jarumar ta bar masana'antar fim tayi aure inda ta Haifa Yara guda biyu mace da namiji. A yanzun haka auren jarumar ya mutu Kuma tana Shirin dawowa masana'antar.

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.
  2. https://www.hausaloaded.com/2021/06/ina-gab-da-dawowa-harkar-film-maryam-abubakar-jan-kunne.html