Masallacin Yamma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masallacin Yamma
masallaci
Bayanai
Farawa 1962
Suna a harshen gida مسجد ياما
Addini Musulunci
Ƙasa Nijar
Zanen gini Falké Barmou (en) Fassara
Tsarin gine-gine Sudano-Sahelian architecture (en) Fassara
Wuri
Map
 14°21′34″N 5°29′57″E / 14.35958°N 5.49922°E / 14.35958; 5.49922
JamhuriyaNijar
Yankin NijarYankin Tahoua
Department of Niger (en) FassaraIlléla (sashe)
Municipality of Niger (en) FassaraBadaguichiri

Masallacin Yaama ( Larabci: مسجد اليمه‎ ) wani masallaci ne da aka gina a cikin tsarin gine-ginen 'yan asalin Sudan-Sahelian, wanda aka gina a shekarar 1962 a Yaama, wani ƙauye a yankin Tahoua, Nijar .

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Ko da bayan fiye da shekaru 60 na mulkin mallaka na Faransa wanda ya ƙare a 1960, yankin ba shi da wani tasiri daga waje. Don haka a lokacin da ƙauyen suka yanke shawarar gina masallacin Juma’a wanda kowa zai hallara domin yin sallah, sai suka zaɓi yin amfani da hanyoyin gargajiya. An gina wannan ginin ne da tubalin laka kuma daga baya gyare-gyaren ya haɗa da gina wata kubba ta tsakiya mai kewaye da hasumiya ta kusurwa huɗu.[1] Kowane ɗan ƙauye ya bayar da gudunmawa;[1] daga mai gidan da ya ba da gudummawar wurin, zuwa ga mutanen da suka yi tubalin laka, da ruwa, tattara itace, da dai sauransu.

Wannan masallacin ya kasance wanda ya samu lambar yabo ta Aga Khan a fannin gine-gine a shekarar 1986.[1]

Gine-gine[gyara sashe | gyara masomin]

An gina masallacin ne da tsarin gine-ginen ’yan asalin Sudan da Sahel, musamman na Tubali da Hausawa ke amfani da shi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]