Masarautar Gokana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Gokana

Masarautar Gokana tana ɗaya daga cikin masarautu shida na mutanen Ogoni a Ogoni (kuma Ogoniland) a yankin Niger Delta na Najeriya . "Masarautar Gokana" tana da abubuwan tarihin ƙasa, na tarihi sannan da kuma na yare daban-daban tare da wasu masu magana da harshen Gokana kimanin 130,000 da ke cikin Karamar Hukumar Gokana a cikin Jihar Ribas . Gokana ta ƙunshi ƙauyuka da dama, ciki har da Lewe, B. Dere, K. Dere, Kpor, Mogho, Bomu, Bodo, Gio-koo, Nwe-ol, Alli D. Bera, Biara, Deeyor, Boghor, Barako da Yeghe.[1][2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Osha, Sanya (2006). "Birth of the Ogoni Protest Movement". Journal of Asian and African Studies. 41 (1–2): 13–38. doi:10.1177/0021909606061746. Archived from the original on 2006-10-17. Retrieved 2010-06-26.
  2. Earlier version of same article.Osha, Sanya (2005). "Birth of the Ogoni Protest Movement" (pdf). Centre for Civil Society, University of KwaZulu-Natal. Retrieved 2010-06-26.[permanent dead link]