Michael Imoudu
Michael Athokhamien Omnibus Imoudu shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ne.
Farko rayuwar da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Michael Imoudu a shekarar 1902, a yankin Afemai na jihar Edo. Mahaifinsa, soja ne a rundunar sojojin Afirka ta Yamma kuma ya'yi aiki a Gabashin Afirka da kuma a Gambiya. Bayan rasuwar iyayensa a shekarar 1922, Imoudu ya rayu kuma ya'yi aiki da wani dan uwansa wanda ya ke aikin layin dogo. Saboda aikin dan uwansa, ya zagaya garuruwa daban - daban a yankin Tsakiyar Yamma da Gabas, a lokacin da yake bakuwa, ya koyi yaren Igbo.[1] Ya halarci makarantu da dama, sannan ya kammala karatunsa na firamare a makarantar gwamnati ta Agbor a shekarar 1927.[2] Ya yi tafiya zuwa Legas a 1928, kuma ya sami aiki bayan shekara guda daya a matsayin ma'aikacin yau da kullun, ya yi kuma aiki a matsayin mai aikin layi a Sashen Post da Telegraph kafin ya shiga layin dogo a matsayin mai koyo.[ana buƙatar hujja]