Nigerian Railway Corporation
Nigerian Railway Corporation | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Gajeren suna | NRC da NR |
Iri | railway company (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Aiki | |
Ma'aikata | 6,516 |
Mulki | |
Hedkwata | Abuja da Lagos |
Tsari a hukumance | state-owned enterprise (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira |
1912 1898 |
Wanda yake bi | Lagos Government Railway (en) da Baro-Kano Railway (en) |
nrc.gov.ng |
Nigerian Railway Corporation hukuma ce ta zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An kirkiri Nigerian Railway Corporation a 1898 lokacin da turawan mulkin mallaka suka samar da hanyoyin jiragen kasa na farko a Nigeria. A October 3, 1912, hukumar jiragen kasa ta Lagos da kuma hukumar jiragen kasa ta Baro-kano suka yi yarjejeniya ta yin hadaka da juna yayin da suka fadada zirga-zirgar su ta zama ta duniya gaba daya wanda kuma suka canja suna zuwa Government Department of Railways. A shekara ta 1955 aka sake canjawa Kamfanin suna izuwa sunan sa na yanzu wato Nigerian Railway Corporation tareda samun cikakkiyar dama ta gudanar da zirga-zirgar su a ko Ina a fadin Nigeria.
Kamfanin ya samu daukaka sosai jim kadan bayan samun yanci a 1964. Bayan wannan lokacin NRC sun sami wata barazana ta ci baya da kuma tabarbarewar kayan aiki na wani lokaci Mai tsawo. Hukumar ta samu karyewa a shekara ta 1988 wanda har takai ga dakatar da zirga-zirga tsawon wata shida. Daga nan aka gyara hanyoyin jiragen a shekara ta 2002 Kuma jiragen suka dawo aiki gadan-gadan kamar a baya. Kamfanin ya sake samun matsaloli daga baya har zuwa 2006 inda aka sake yin gyararrakin hanyoyi da kuma samar da sababbin tsare-tsare abisa taimakon kasashen waje.
NRC ta sami matsaloli na karayar tattalin arziki fiye da sau daya a shekara ashirin da ta gabata. Rashin inganta kayan aiki da kuma yawan ma'aikata ya bada gudun mawa wajen karyewar kamfanin. A shekara ta 2015 bayan wasu tsare-tsare da akai tayi an takaita zirga-zirgar jiragen izuwa sau hudu a sati, zuwa Kano sau biyu, zuwa Jos sau daya da Kuma zuwa Maiduguri sau daya.