Miyar kuka
Miyar kuka | |
---|---|
miya | |
Kayan haɗi | baobab leaf (en) da Manja |
Tarihi | |
Asali | Najeriya da Arewacin Najeriya |
Miyar kuka, ana kuma kiranta da luru, su kuma Fulani suna kiranta da (ɓokko), miya ce daga cikin irin abinci na mutanen Arewacin Najeriya da Kudancin Nijar. Ana samar da miyar ne daga garin kuka wanda ake samu daga bishiyar kuka.[1] Ana hada ta da Tuwon Masara, Tuwon shinkafa ko Tuwon Dawa.[2] ne na musamman.[3][4][5]
Amfanin miyar kuka
[gyara sashe | gyara masomin]Kamin masanan Kimiyya su yi nazarin alfanonin dake cikin miyar kuka, an dauki lokaci mai tsawo ana amfani da ita a kasashe da dama a matsayin miya wacce aka fi sani kuma aka fi gasgatawa. Sai kimiyya ta zo ta bada na ta gudummuwa wacce ta yi bayani daki-daki dangane da dimbin amfanin miyar kuka. Ga kadan daga cikin su:[6]
Muhimmancin Miyar Kuka
[gyara sashe | gyara masomin]Miyar kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya. Akwai sinadaran carbohydrate masu baiwa jikin dan adam kuzari, akwai natural sugars wacce ba ta da wani illa ko lahani ga jikin ko wane mutum, akwai proteins wadanda sune ke gina jiki, akwai carotenes, riboflabin, Bit-C, Minerals, potassium, iron, magnesium, manganese, phosphorus, zinc, calcium, glutamic, catechins, tertrate, rhamnose, glutamic acid da sauransu. Miyar kuka tana taimakawa sosai ga mai fama da basir, tana maganin wannan ciwon musamman ga wanda basir ya taba wa hanjin ciki inda zai haifar da todins na kwayar cutar bacteria ta E.coli wanda ciwon ciki zai addabi mutum da yawan da tusa mai wari da kumburin ciki. Miyar kuka na dauke da sinadaran Iron masu kara yawan jini fiye da wadanda ke a cikin nama. Kenan shan miyan kuka indai sinadaran Iron ake nema yafi cin nama. Miyar kuka na dauke da sinadaran Bitamin C masu yawan gaske dan haka idan ana neman sinadaran bitamin C to ba dole bane sai an sha lemu sai a fake shan miyan kuka za ta wadatar. Miyar kuka na kara kaifin basira, wannan wata hikima ce ta daban domin a hakika na kula da cewa mutanen da suke amfani da miyan kuka basirar su ta dara ta wadanda ba su amfani da ita. Nima na lura idan ina shan miyan kuka to karfin basira ta ya kan karu. Miyar Kuka na dauke da sinadaran calcium fiye da wadanda ke a cikin madara. Miyar kuka na wanke dattin ciki daga cushe-cushe, kusan ita kadai za ka sha ka konta kuma ka ta shi ka ji cikinka wasai ba kumburi ba tusa ba zafin ciki ba gudawa ba tashin zuciya, ba kaikayin jiki ko tsamin ciki.[7][3]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Adamu, Abdalla Uba, 1956-, Adamu, Yusuf Muhammad., Jibril, Umar Faruk. Hausa home videos : technology, economy and society. Kano, Nigeria: Center for Hausa Cultural Studies. 2004. ISBN 978-36906-0-4.OCLC 61158034.
- Abubakar Aliyu Mohammed. Cultural Torism. ISBN:978-978-087-937-2
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "KUKA SOUP". Online Nigeria. 19 February 2003. Archived from the original on 24 September 2015. Retrieved 6 July 2015.
- ↑ "Miyan Kuka (Baobab Leaf Soup)". Terry Adido. Grated Nutmeg. 18 June 2014. Retrieved 6 July 2015.
- ↑ 3.0 3.1 https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54203041
- ↑ https://cookpad.com/ng-ha/recipes/9529970-tuwo-da-miyar-kuka
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-kasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
- ↑ "Miyan Kuka (Baobab Leaves Soup)". All Nigerian Recipes (in Turanci). Retrieved 2020-05-11.
- ↑ http://bashirhalilu.blogspot.com/2018/07/amfanin-bishiyar-kuka.html?m=1