Mohammed Daggash

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Daggash
Minister of Works and Housing (en) Fassara

6 ga Afirilu, 2010 - 2011
Hassan Muhammed Lawal - Mike Onolememen (en) Fassara
Minister of Budget and National Planning (en) Fassara

ga Yuli, 2007 - Oktoba 2008 - Shamsuddeen Usman
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007
District: Borno North
Rayuwa
Haihuwa 22 Disamba 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Kwaleji ta Landon
Jami'ar Ahmadu Bello
King's College, Lagos (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Masanin gine-gine da zane
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Mohammed Sanusi Daggash ya kasance (an haife shi a ranar 22 ga watan disemban 1960) injiniya ne mai zane, Masanin tattalin arziki kuma dan kasuwa dan Najeriya wanda aka zaba a matsayin dan majalisan Dokoki na Kasa a shekarar 1999, kuma ya zama sanata a Arewacin Borno (Jihar Borno) a shekarar 2003. Tsohon shugaba Umaru Musa ya nada shi a matsayin ministan tsari na kasa (National Planing Commission of Nigeria) a watan Julin shekarata 2007,ya kuma sauke shi daga wannan matsayin a Oktoban shekarar 2008.An kara nadashi ministan ayyuka a shekara ta 2010.

Farkon Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mohammed Sanusi Daggash a ranar 22 ga watan Disemban 1960 a Kironewa, karamar hukumar Marte a Jihar Borno.[1] Ya halarci Capacity School dake Kaduna (1966-1973) saikuma Kings College Lagos (1973-1978). Ya kuma halarci Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria a 1978, ya sama digiri na Masters a zanen gidaje a 1984. Dagash yayi bautar kasa (N.Y.S.C) a Ministry of Works and Housing dake Kaduna daga (1984-1985). A shekarar 1985 ya zama ya sama tallafin karatu na comonwealth zuwa Jami'ar University, College dake Landan ya sami Mastas digiri a Developemt Econics a 1986.[2] Ya kuma halarci Karatun gaba na Jami'ar Havard a 1988.

Ya dawo Najeriya a 1986, Daga ya kirkiro Consultancy Firm (Mass consult - Najeriya) a Kaduna. A 1989 an zabeshi cikin Board na Kungiyar Yan Wasan Kwallon Kafa na Najeriya na tsawon shekaru hudu. Yayi ayyuka a wurare da dama har zuwa lokacinda ya shiga dan koron Sani Abacha. A 1995 ya fara karatunsa na Mastas a Public Administration an kuma bashi sakamako a 1998. An zabeshi matsayin dan majalisar kasa na Marte, Monguno da kuma Ngazi na jihar Borno a 1999.[2].

Matsayin Sanata[gyara sashe | gyara masomin]

Ya fito takara a matsayin a jam'iyyar PDP kuma an sanar cewa ya zama sanata daga shekarar (2003-2007) mai walkilta Arewacin Borno.[3] Abokiyar adawarsa Hajiya Fatima Ibrahim Bulama ta kai kararsa akan bata yadda da sakamakon zaben ba.[4] haka Kotu ta tsaida Dagash a Nuwanban 2003, daga baya kotu ta tabbatarda rashin chanchanta Fatima Bulama a matsayin Sanata, haka aka sake zabe[5] daga baya Dagash ya koma matsayinsa na sanata.[6]

Dagash yayi aiki har na rassa dababn daban har guda Goma a fanni daban daban na Kwamitin Sanatoci a lokainsa.[7] Shi ne mataimakin Chairman na Kwamitin Sanatoci a fannin Kidaya da Katin dan kasa, kuma memba ne na Kwamitin Birnin Tarayya Abuja, Masu bada basuka da kuma Parliamentary Network On World Bank (PNWB). Har wayau memba ne na Board of Directors na Guinea Insurance Comapany.[8]

Shine dan takarar jam'iyyar PDP a Afrilun 2007, a zaben 'yan majalisar Dattawa, ta Kada a Arewacin Borno, amma daga baya ya janye saboda zanga zanga da mabiya ANPP sukayi saboda murdiya a zaben. Daga baya dan takarar jam'iyyar ANPP Maina Ma'aji ya lashe kujerar.[9][10]

Ayyukansa daga Baya[gyara sashe | gyara masomin]

An zabe Daggash matsayin Minista na National Planning a Julin 2007.[11] Yana cikin dyan koran da Shamsuddeen Umar ya jagoranta a zuwa kasar Chena a watan Febrerun 2008.[12] A Octoba 2008, Dagash ya sanar cewa Najeriya ta yanke kasafin mai a matsayi dalar Amurka 45 duk barrel daya, dalilin faduwar darajan manfetur a duniya.[13]

A shekarar 2008, Daggash ya zama Darekta na Effectivo Capita, Kamfanin sanya. Hannun jari dake Abuja.[14]

A watan Nuwanban 2009, Dagash yana cikin masu hannun jari a kungiyar tawaye ga manyan jam'iyyar PDP na Borno don sukar Charirman na fati da wasu mana a jihar.[15]

An nada Daggash matsayin Minista ayyuka da raya Birane a ranar 6 ga watan Aprelu, shekara ta 2010.[16]

.

Kara dubi[gyara sashe | gyara masomin]

  • List of Nigerian architects.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 

  1. "Senator Mohammed Sanusi Daggash - CV". Archived from the original on 27 July 2011.
  2. 2.0 2.1 "Senator Mohammed Sanusi Daggash". Mohammed Sanusi Daggash.Archived from the original on 2010-12-08. Retrieved 2009-12-25.
  3. "Michael Olugbode (26 February 2009). "When Will Borno PDP Wake From Slumber?". This Day. Retrieved 2009-12-25.
  4. "Funmi Peter-Omale (2003-12-22). "Daggash: Going Back to Voters..." ThisDay. Archived from the original on 2005-11-28. Retrieved 2009-12-25.
  5. "Isa Umar Gusau (June 1, 2004). "INEC defies courts on Borno senatorial election". Daily Trust. Retrieved 2020-06-09
  6. "Ise-Oluwa Ige (March 31, 2006). "Lawyers' strike, a blemish on Obasanjo's govt". Vanguard. Retrieved 2009-12-25.
  7. "WE WELCOME OUR GUEST SPEAKERS TO THE NIGERIA-CANADA CONFERENCE 2008". NIDO Canada. Archived from the original on 2009-10-29. Retrieved 2020-06-09.
  8. "Our Board of Directors". Guinea Insurance Company. Retrieved 2020-06-09.
  9. "INDEPENDENT NATIONAL ELECTORAL COMMISSION NOMINATED CANDIDATES FOR ELECTION TO THE SENATE 2007" (PDF). Radio Nigeria. Archived from the original (PDF) on 2011-05-31. Retrieved 2009-12-25
  10. "Sen. Maina Maaji Lawan". National Assembly of Nigeria. Archived from the original on December 22, 2008. Retrieved 2020-06-09
  11. "Yar'Adua names cabinet". Africa News, 27 July 2007. Archived from the original on 28 September 2011.Retrieved 2009-12-25
  12. "Vice Minister Yu Meets Delegation of Nigeria".Ministry of Commerce of the People's Republic of China. 2008-03-03.Retrieved 2020-06-09.
  13. "Nick Tattersall (Oct 20, 2008)."Nigeria cuts benchmark oil price to $45 in '09 budget". Reuters. Retrieved 2009-12-25.
  14. "About Efectivo - Our People". Efectivo Capital. Retrieved 2020-06-09.
  15. "Muideen Olaniyi (18 November 2009). "Daggash, Mustapha, Others Unite Against Ciroma". Daily Trust (Abuja). Retrieved 2020-06-09.
  16. "Factbox: Nigeria's new cabinet ministers". Reuters. Apr 6, 2010. Archived from the originalon 2010-04-10. Retrieved 2021-06.09