Jump to content

Moncef Ben Salem

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Moncef Ben Salem
Lua error a mw.lua, layi na 656: invalid value (nil) at index 1 in table for 'concat'.
Minister of Higher Education (en) Fassara

24 Disamba 2011 - 29 ga Janairu, 2014
Member of the 2011 Constituent National Assembly (en) Fassara

22 Nuwamba, 2011 - 28 ga Faburairu, 2012
District: Q16670951 Fassara
Election: 2011 Tunisian Constituent Assembly election (en) Fassara
Minister of Higher Education (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa1 ga Afirilu, 1953
ƙasaFrench protectorate of Tunisia (en) Fassara
Tunisiya
Mutuwa24 ga Maris, 2015
Karatu
MakarantaUniversité de Toulouse (mul) Fassara
Sana'a
Sana'amasanin lissafi, ɗan siyasa da Malami
EmployersUniversity of Maryland (en) Fassara
Imani
AddiniMusulunci
Jam'iyar siyasaEnnahda Movement (en) Fassara
Moncef Ben Salem

Moncef Ben Salem ( Tunisian Arabic; Fabrairu 1, shekarar alif 1953 - Maris 24, shekarar alif 2015) ɗan siyasan Tunisiya ne kuma malamin jami'a. [1] [2] Ya taɓa zama ministan ilimi mai zurfi da bincike na Kimiya a karkashin firaminista Hamadi Jebali. [3]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Moncef Ben Salem a ranar 1 ga watan Afrilu shekarar alif 1953. Ya sami digiri na BA a fannin lissafi da Physics a shekara ta alif 1972 sannan ya yi digiri na biyu a fannin lissafi a shekara ta alif 1974.[4][5][6] Ya sami digirin digirgir a fannin lissafi da Physics daga Jami'ar Toulouse da Supméca a birnin Paris.[4][5][6] Ya kasance memba na Ƙungiyar Union of Arab Mathematicians and Physicians daga shekarar alif 1980 zuwa shekarar alif 1987. Shi ne ya kafa Ecole Nationale d'Ingénieurs de Sfax a cikin shekara ta alif 1983[7]

Harkar siyasa da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]
Moncef Ben Salem

Ya kasance ɗan ƙungiyar Ennahda Movement. Ya yi suka ga shugabannin Habib Bourguiba da Zine El Abidine Ben Ali, yana mai kiran Bourguiba a matsayin "Zionist". Sakamakon gwagwarmayar siyasarsa ƙarƙashin Ben Ali, an daure shi na tsawon watanni goma sha takwas daga shekarar alif 1987 zuwa shekarar alif 1989, kuma daga shekarar alif 1990 zuwa shekarar alif 1993. A shekara ta alif 1987, an soke fasfo ɗinsa, kuma an hana shi fita daga Tunisia ko tafiya cikin kasar tsawon shekaru ashirin, kamar yadda 'ya'yansa suka yi.[4][8][9] Daga shekarar alif 1993 zuwa shekarar alif 2011, an tilasta masa zama a ƙarƙashin sa ido (Surveillance). An kuma hana shi aiki a matsayin malamin jami'a. A lokacin waɗancan shekarun, an tallafa masa da Kwamitin Masana'antu da kuma al'ummar ilmin lissafi na Amurka. Daga baya ya koyar a Jami'ar Maryland da ke Amurka, a Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Faransa a Faransa, Italiya, Jamus, Belgium, da Jami'ar Sfax da ke Tunisiya.

Moncef Ben Salem a tsakiya

A ranar 20 ga watan Disamba, shekarar alif 2011, bayan an hambarar da tsohon shugaban ƙasa Ben Ali, ya shiga majalisar ministocin Jebali a matsayin ministan ilimi mai zurfi. [6]

Ya rasu a ranar 24 ga watan Maris, shekarar alif 2015, ya bar bazawara da ‘ya’ya 4.[4][10][11]

  1. ↑ (in French) Babnet Dec'24th 2011
  2. ↑ leaders.com: Moncef is named a professor again
  3. ↑ CIA World Leaders
  4. 1 2 3 4 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named "leaders".
  5. 1 2 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named "agence".
  6. 1 2 3 Dr. Moncef Ben Salem to visit the Fields Institute, Fields Institute, 20 March 2012
  7. ↑ "Moncef Ben Salem nommé professeur de l'enseignement supérieur". Leaders (in Faransanci). Retrieved 2017-11-16.
  8. ↑ (in French) Death of Moncef Ben Salem Archived 2015-04-02 at the Wayback Machine Business News March 24, 2015
  9. ↑ (in Larabci)
  10. ↑ (in French) Death of Moncef Ben Salem Archived 2015-04-02 at the Wayback Machine Business News March 24, 2015
  11. ↑ (in Larabci)