Mr. P (mawaƙi)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mr. P (mawaƙi)
Rayuwa
Cikakken suna Peter Okoye
Haihuwa Jos, 18 Nuwamba, 1981 (42 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Ahali Paul Okoye
Sana'a
Sana'a mawaƙi, YouTuber (en) Fassara, singer-songwriter (en) Fassara da mai tsara
Mamba P-Square
Artistic movement rhythm and blues (en) Fassara
Afrobeats
electronic dance music (en) Fassara
contemporary R&B (en) Fassara
Peter Okoye

Peter Okoye wanda aka fi sani da Mr P ko P-square (An haife shi ranar 18 ga watan Nuwamba, 1981). Ya kasance mawaki ne a Najeriya.[1] Ya yi suna a shekarun 2000s a matsayin memba na P-Square duo, tare da ɗan'uwansa ba-tagwaye Rudeboy,[2] kuma a cikin 2021 an ba shi digiri na girmamawa daga Jami'ar ESCAE a Jamhuriyar Benin.[3][4]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Mista P da Rudeboy tagwaye ne, sun taso ne a babban iyali, a birnin Jos a jihar Plauteau, Najeriya. An haife shi a cikin dangin Josephine Okoye da Mazi Moses Okoye.[5]

Peter da ɗan'uwansa Paul sun shiga makarantar kiɗa da wasan kwaikwayo, inda suka fara rawa, rera waƙa da kuma kwaikwayon waƙoƙin, shahararrun mawaƙa Irin su; MC Hammer, Bobby Brown da Michael Jackson.[6]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin 2017, ƙungiyar P-Square ta watse kuma membobin ƙungiyar biyu sun raba gari (sun rabu).[7][8] Mista P ya fitar da kundin sa na farko (solo single) mai taken "For my Head", "Cool It Down" a shekarar 2017.[9]

A cikin 2018 Mista P yayi haɗingwiwa da Nyanda na Brick & Lace, acikin wata waƙa mai suna "Wokie Wokie".[10] A cikin 2021, Mista P ya kafa kamfanin waƙar sa mai suna (PClassic Label), kamfanin rikodin ɗin nasa, ya rattaba hannu kan ɗan gwagwarmayar Najeriya da disc jockey DJ Switch[11] kuma a cikin 2021, ya fitar da kundi na farko na 16 mai suna, The Prodigal wanda ya fito da mawaka irin su Tiwa. Savage, Simi, Teni, Wande Coal, Tamar Braxton, Singah, Mohombi, DJ Switch, da OvieKelz.[12][13]

Yarjejeniya[gyara sashe | gyara masomin]

Peter Okoye wajen aiki

A ranar 16 ga Yuni, 2016, Mr P ya zama jakadan motar Kia.[14] An kuma naɗa Mr. P a matsayin jakadan alama na madarar Olympic, wanda kamfanin (Nutricima Limited) ta samar.[15] Peter ya kafa wani shiri mai suna Dance with Peter na Gidan talabijin ɗin reality TV show, wanda kamfanin Globacom Telecommunication Limited ke ɗaukar nauyin shirin.[16] A cikin watan Agusta 2021, an bayyana shi a matsayin jakadan alama na Adidas, kamfanin masana'antu wanda ke hulɗa da takalma, tufafi da sauransu.[17]

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 17 ga Nuwamba 2013 ya yi aure, kuma auren ya gudana ne a cikin jirgin ruwa a Lekki, Lagos, Najeriya.[18] Yana da ɗiya, mai suna Aliona [19]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Obinna (2020-12-19). "Mr P (Peter Okoye) Biography: Early life, PSquare, solo career and facts". Sidomex Entertainment (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  2. Stets, Regina (2020-11-20). "Peter Okoye's biography and solo career". Legit.ng (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  3. Ekaete, Bassey (2021-06-25). "Mr P bags honorary doctorate degree | The Nation Nigeria". The Nation (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  4. Edeme, Victoria (2021-06-24). "Benin Republic varsity confers honorary doctorate on singer Mr P". The Punch (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  5. Muoka, Chidera (2017-11-19). "Mr P: Singer, Dancer, Family Man". The Guardian (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  6. Katsikas, Paula (2013-07-30). "P-Square's 'Personally' Tribute To Michael | Michael Jackson World Network". The Michael Jackson World Network (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  7. Durosomo, Damola (September 26, 2017). "Here's What We Know About P-Square's Absurdly Messy Breakup". OkayAfrica. Retrieved March 2, 2022.
  8. Awojulugbe, Oluseyi (2016-03-14). "PSquare's Peter goes solo... after 19 years". TheCable (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  9. "Mr. P - For My Head". DCLeakers.com (in Turanci). 2017-11-20. Retrieved 2021-07-29.
  10. "Mr P Teams Up With Nyanda Of Brick & Lace For 'Wokie Wokie' (Video)". Concise News (in Turanci). 2018-08-24. Retrieved 2021-07-29.
  11. "Peter Okoye signs new artist on label P Classic Records". Vanguard. December 18, 2017. Retrieved March 2, 2022.
  12. Ige, Tofarati (2021-04-03). "Mr P releases debut solo album 'Prodigal'". The Punch (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  13. Okirike, Nnamdi (2021-05-17). "Mr. P Sets Out To Blaze His Own Trail With 'The Prodigal'". OkayAfrica (in Turanci). Retrieved 2021-07-29.
  14. Bridget (2016-06-16). "Peter Okoye Signs New Deal With KIA". The Guardian (in Turanci). Retrieved 2021-08-28.
  15. Dawodu, Adebayo (October 25, 2014). "P-Square's Peter Okoye Opens Up On His Deal As Olympic Milk Brand Ambassador". The Nigerian Voice. Retrieved March 2, 2022.
  16. "Glo Dance with Peter: Kelvin, Miracle, 3 others on probation". Vanguard News (in Turanci). 2015-12-06. Retrieved 2021-08-28.
  17. "China and EU sign landmark climate deal". Climate Change and Law Collection. doi:10.1163/9789004322714_cclc_2015-0174-008. Retrieved 2021-08-28.
  18. "Peter Okoye of PSquare gets hitched!". Capital FM (in Turanci). 2013-11-20. Retrieved 2022-01-31.
  19. "Peter Okoye of PSquare gets hitched!". PM News Nigeria (in Turanci). 2013-01-22. Retrieved 2022-01-31.