Nabila Rabiu Zango

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Nabila Rabiu Zango, 'yar asalin garin Zangon-Daura Karamar Hukumar Zango, ce da ke a Jihar Katsina Najeria. An haife ta a ranar 19 ga watan Agustan,shekara ta alif dari tara da tamanin da tara 1989 a ƙaramar hukumar Funtua dake a Jihar Katsina [1]. Shahararriyar marubuciyar littafan hausa ce wadda ake ma lakabi da Marubuciyar Zamani. Ta halarci taron ƙara sani  (workshop) akan harkar rubutu da dama, a ciki akwai wanda tayi a karkashin kungiyar MacArthur foundation (KILAF2022), Kannywood foundation 2022, Ta fara rubutun littafin hausa a shekarar 2015. Cikin litattafan da ta rubuta sun haɗa da:

  1. Agola.
  2. Shatu ɗiyar Maharbi.
  3. A maƙabarta Aka Haife ni.
  4. Rayuwar Mata Ayau.
  5. Kafin In Zama Lauya.
  6. Darajar Muhalli.
  7. Kowa ya Taka Dokar Allah.
  8. Ƴaƴan mu Amanar Mu.
  9. Matasan Mu.
  10. A Wani Gida.
  11. Almajirai Ma Ƴaƴa ne.
  12. A Wata Makaranta.
  13. Mai Nasara.
  14. Mata Jigon Alumma.
  15. Na Shiga Ban ɗauka ba.
  16. Waye Ne.
  17. Ba ni Ba ne.
  18. Alƙali ne.
  19. Daga Baya Kenan.
  20. Halinta Ne.
  21. Burin Ɗan Adam.
  22. Darasi Ne.
  23. Ajalinta Ne.

A halin yanzu ta koma harkar rubutun fina-finai (screenplay). Daga cikin finafinan da ta rubuta akwai babban shirin nan mai dogon Zango wanda aka fi sani da ALAQA,  akwai DALA-DALA, akwai SIRRIN BOYE,  KE DUNIYA, BINTU. Ta rubuta ƙananun finafinai irin su RANA DUBU,  MARWANATU,  LABARIN MAIMUNATU da sauransu.

Nabila Rabiu Zango, Mace ce mai kaifin basira, hazaƙa, kyauta da fara'a, da son gyaruwar al'umma musamman Matasa. Tana da sha'awar koyarwa,  bincike da kallon fina-finai da kuma rubutu akan Matasa.

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ta yi karatun Firamare a Model Primary School Funtua daga shekara ta alif 1995-2000. Ta kuma yi Sakandare a Government Girls Secondary School Malumfashi inda ta gama a shekarar 2006. Ta cigaba da karatu daga shekara ta 2008 a Isa Kaita College Of Education Dutsin-ma har zuwa sheakara ta 2011.

Mukami da Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

A halin yanzu  tana aikin koyarwa a makarantar Firamare da ke a ƙaramar hukumar Zango ta Jihar Katsina.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]