Nicolas Chumachenco

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nicolas Chumachenco
Rayuwa
Haihuwa Kraków (en) Fassara, 27 ga Maris, 1944
ƙasa Poland
Mutuwa Schallstadt (en) Fassara, 12 Disamba 2020
Ƴan uwa
Ahali Ana Chumachenco (en) Fassara
Karatu
Makaranta Curtis Institute of Music
University of Southern California (en) Fassara
USC Thornton School of Music (en) Fassara
Harsuna Polish (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a violinist (en) Fassara
Kayan kida goge

Nicolas Chumachenco ko kuma Chumachenko (27 Maris 1944 - 12 Disamba 2020) ɗan asalin kasar Poland ne mawakin violin na solo, farfesa, kuma darektan ƙungiyar mawaƙa ta Chambar Sarauniya Sofia.[1] Ya lashe lambar yabo ta Diploma Konex Award a shekarar alif 1999, a matsayin ɗaya daga cikin Mawakan Bow na musamman na tsawon shekaru goma a Argentina.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Chumachenco a Kraków, a Poland inda sojojin Nazi suka mamaye, ga iyayen ‘yan kasar Ukraine da suka bar Poland a ƙarshen yakin duniya na biyu. Ya girma kuma ya fara koya kiɗa a Argentina . Chumachenco ya bar Argentina don yin karatu a Amurka a Makarantar kiɗa ta Thornton ta Jami'ar Kudancin California tare da Jascha Heifetz sannan daga baya a Cibiyar Curtis da ke Philadelphia tare da Efrem Zimbalist kuma ya sami lambobin yabo a gasar Tchaikovsky ta duniya da gasar kiɗa ta Sarauniya Elisabeth.[2]

Chumachenco ya kasance dan wasan violin na farko a Zurich Quartet, farfesan violin a Hochschule für Musik Freiburg sannan ya yi aiki a matsayin jagora kuma daraktan kiɗa na kungiyar kade-kade ta Sarauniya Sofía Chamber a Madrid .

Ana ('yar'uwa), Nicolas da Eric (ɗa) Chumachenco a Würzburg, 14 ga Fabrairu 2018. Hoton Tamara Hegedüs.

Ya rasu a Schallstadt, Jamus.

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

'Yar'uwarsa Ana Chumachenco (an haife ta a 1945) farfesa ce itama ta violin a Hochschule für Musik und Theater Munich . Ɗansa Eric Chumachenco (an haife shi a shekara ta 1964) ɗan wasan fiyano ne na gargajiya kuma yana koyarwa a Jami'ar Mozarteum Salzburg.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Nicolás Chumachenco - Concertino Director". Festival Internacional de Música "Ciudad de Ayamonte". Archived from the original on 26 July 2011. Retrieved 4 August 2009.
  2. Juan Antonio Torres Planells. "Nicolas Chumachenco, violin". Grijalvo. Retrieved 4 August 2009.
  3. "Eric Chumachenco". Mozarteum Salzburg. Archived from the original on 25 September 2020. Retrieved 10 June 2017.