Nigerian braille
Kiwon zomaye a Nigeria
Kiwon zomaye (wanda ake kira cuniculture da Turanci), na nufin haihuwa da kiwon zomaye don nama, fata, ko kuma matsayin dabbar shakatawa. A Najeriya, kiwon zomaye yana samun karbuwa saboda karancin kudin fara yinsa, yawan haihuwa, da kuma karancin kitsen naman sa.(lean meat)
2.Dalilan Da Yasa Kiwon Zomaye Ke Karbuwa a Najeriya
Kananan kudin fara kiwon idan aka kwatanta da kaji ko shanu.
Gaggawar girma da yawan haihuwa: Zomo na iya haihuwa sau 6 zuwa 8 a shekara, yana haifar da 'ya'ya 6 zuwa 10 a kowane lokaci.
Yawan bukatar naman zomo: Nama ne fari, mara mai da sinadarin cholesterol.
Baya bukatar fili mai yawa: Ana iya kiwon su a gida ko cikin kwantena kanana.
Cibiyar samun kudin shiga da abinci mai gina jiki ga iyalai da manoma kanana.
3.Irin Zomayen da Ake Kiwowa a Najeriya(Breeds)
Wadannan su ne ire-iren zomayen da aka fi kiwo a Najeriya saboda jurewar su da kuma yawan haihuwa:
a. New Zealand White
Launi: Fari qal da idanu ja.
Amfani: Ana kiwon sa ne don nama.
Siffofi: Yana girma da sauri, mai girma, kuma uwa mai kyakykyawan kulawa da ‘ya’ya.
b. Chinchilla
Launi: Fari da launin toka.
Amfani: Nama da fata.
Siffofi: Matsakaicin girma zuwa babba, nama mai kyau.
c. Californian
Launi: Jiki fari, hanci, kunne, kafa da wutsiya baki.
Amfani: Don samar da nama.
Siffofi: Yana girma da sauri kuma yana cin abinci da kyau.
d. Flemish Giant
Launi: Launuka daban-daban (toka, fari, rairayi, baki).
Amfani: Don nama da nune-nune.
Siffofi: Babban jiki sosai, amma yana daukar lokaci kafin ya balaga.
e. Dutch
Launi: Fari da baki da aka raba.
Amfani: Mafi yawa ana kiwon su a matsayin dabbar shakatawa ko don bincike.