Olajumoke Okoya-Thomas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Olajumoke Okoya-Thomas
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

3 ga Yuni, 2003 -
Rayuwa
Haihuwa 20 ga Janairu, 1957 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Mahaifi Molade Okoya-Thomas
Karatu
Makaranta Makarantar Kasuwanci ta Harvard.
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Alliance for Democracy (en) Fassara

Olajumoke Abidemi Okoya-Thomas mamba ce a Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya.[1]Ta kasance 'yar jam'iyyar All Progressives Congress kuma tana wakiltar mazabar Lagos Island I Mazabar Tarayyar Lagos, Najeriya .[2]

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kasance 'ya ga Cif Molade Okoya-Thomas,[3] Asoju Oba na Legas, an haife ta a ranar 20 ga Janairu 1957. Tana da difloma a fannin gudanar da Gwamnati (Senior Managers in Government) daga Jami'ar Harvard da difloma a sec. gudanarwa daga Kwalejin Burleigh.[4]

Harkar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Olajumoke Okoya-Thomas ta fara aiki ne a ranar 29 ga Afrilun 2011 a karo na uku a jere a majalisar wakilan tarayya. Ra'ayoyin ta na doka da shari'a sun ta'allaka ne akan cigaban zamantakewar Mata da kananan yara.[5] A yanzu haka ita ce Shugabar kwamiti a kan Siyarwar Jama'a sannan kuma mamba ce a kwamitin "Banking & Currency, Diaspora, Niger Delta", da kuma kwamitin Mata a majalisa.

Ita ce tsohuwar shugabar kwamitin gidan yarin.[6]

Olajumoke Okoya-Thomas ta dauki nauyin kudirin doka kan tilasta shayar da jarirai nono a shekara ta 2013. Kudirin ya gaza saboda wakilan sun dage kan cewa batu ne da ya fi dacewa a bar shi a bainar jama'a saboda "babu macen da za a tilasta mata shayar da danta nono" duk da cewa sun amince da fa'idodin lafiya na shayar da nonon wanda ba a iya jayayya da hakan.[7] Har wayau, ita ce kuma shugabar mata na jam’iyyar All Progressive Congress a jihar Legas.[8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Public offices held by Olajumoke Abidemi Okoya-Thomas in Nigeria". citizensciencenigeria.org. Retrieved 5 April 2022.
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2014-03-29. Retrieved 2020-11-22.
  3. "Jumoke Okoya Runs Into Political Trouble For Eyeing Remi Tinubu's Senatorial Seat!". Society Now Nigeria. Archived from the original on 31 March 2014. Retrieved 29 March 2014.
  4. "Olajumoke Okoya-Thomas". Nnu.ng - Nigeria News Update. Retrieved 22 February 2022.
  5. "OLAJUMOKE OKOYA-THOMAS Politician Profile Page". Shine Your Eye. Retrieved 29 March 2014
  6. "Members Federal House of Representatives". Nigerian National assembly. Retrieved 29 March 2014.
  7. "Reps Reject Bill On Exclusive Breast Feeding". Channels TV. 29 January 2013. Retrieved 29 March 2014.
  8. Admin. "Lagos APC: Jumoke Okoya-Thomas task party leaders on Kemi Nelson's conduct | National Daily Newspaper". Retrieved 27 August 2019.