Olamijuwonlo Alao Akala
Olamijuwonlo Alao Akala | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 9 Satumba 1984 (40 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Olamijuwonlo Alao Akala (an haife shi (1984-09-09 ) [1] ɗan siyasar Najeriya ne kuma ɗan majalisar wakilai na yanzu a majalisar wakilai ta ƙasa ta 10, mai wakiltar mazaɓar Ogbomoso ta arewa, ta kudu da Orire tun a watan Yuni 2023. [2] Shi ne Shugaban Kwamitin Matasa na Majalisar Wakilai a Majalisar. [3] Olamjuwonlo, wanda kuma ɗa ne ga tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Adebayo Alao-Akala, ya riƙe muƙamin Shugaban Ƙaramar Hukumar Ogbomoso ta Arewa daga shekarun 2018 zuwa 2019. [4]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Olamjuwonlo Alao-Akala, ɗane[1] na farko ga marigayi Otunba Adebayo Christopher Alao-Akala, tsohon gwamnan jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya, ya yi karatunsa a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Ogbomoso, da Kwalejin Rainbow da ke Surulere, Jihar Legas. Daga nan ya sami digiri na farko a fannin Computer and Information Science a Jami’ar Lead City, Ibadan, a shekarar 2008. Daga baya, ya sami digiri na biyu a fannin Gudanar da Sabis daga Jami'ar Buckingham, United Kingdom. Yana auren Hadiza Okoya, ɗiyar wani ɗan kasuwa Cif Razaq Akanni Okoya. [5]
Aikin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Shahararriyar siyasar Olamju ta fito ne a shekarar 2017 lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Marigayi Sanata Abiola Ajimobi ya naɗa shi Shugaban riƙo na Ƙaramar Hukumar Ogbomoso ta Arewa. Daga baya ya tsaya takara kuma ya lashe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar a ranar 12 ga watan Mayu, 2018. A shekarar 2023, an zaɓi Olamju a matsayin ɗan majalisar wakilai ta ƙasa, mai wakiltar mazaɓar Ogbomoso ta arewa, ta kudu, da Orire a majalisar wakilai, inda yake riƙe da muƙamin shugaban kwamitin matasa na majalisar wakilai. [6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Olamijuwonlo Alao-Akala". StateCraft Inc. 2023-09-27. Retrieved 2024-11-20. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name "f595" defined multiple times with different content - ↑ Ibeh, Ifeanyi (2023-06-13). "Olamijuwonlo Alao-Akala – The Dawn of Greatness". The Guardian Nigeria News. Retrieved 2024-11-20.
- ↑ Chukwuajah, Nchetachi (2024-10-08). "Constitutional change necessary for national development". Tribune Online. Retrieved 2024-11-20.
- ↑ "Oyo govt sacks Akala's son as local govt chair". The Nation. 2019-02-20. Retrieved 2024-11-20.
- ↑ John, Beloved (2024-01-28). "SOFT SIDE: Rep celebrates wife's birthday on social media". OrderPaper. Retrieved 2024-11-20.
- ↑ "Oyo: Ajimobi nominates nephew, Akala's son as LG caretaker chairmen – The Sun Nigeria". The Sun Nigeria. 2017-04-05. Retrieved 2024-11-20.