Omololu Falobi
Omololu Falobi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 20 century |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | Lagos,, 5 Oktoba 2006 |
Yanayin mutuwa | kisan kai |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida |
Omololu Falobi ( 1971-5 ga watan Oktoba, 2006) ɗan jaridar Nijeriya ne, kuma mai gwagwarmaya da cutar kanjamau. A 1997, ya kirkiro JAAIDS. [1] Kyautar Omololu Falobi an kirkireshi ne da sunan sa.[2]
A shekarar 1998, ya kirkiro kungiyar JAAIDS, wata kungiya ce mai zaman kanta wacce ta hada ‘yan jaridu daga sassan kasar nan domin wayar da kan jama’a game da illolin cutar kanjamau da kuma yadda za a kiyaye daga cutar.[3] A cikin 2004 da 2005, ya kasance wakili a kwamitin Hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau wato Joint United Nations Programme on HIV/AIDS.[4]An kashe shi a ranar 5 ga Oktoba, 2006 a Legas, da misalin karfe 10 na dare; bai dade da barin hedikwatar kungiyar sa da ke Legas ba. An yi zargin cewa wadanda suka kashe shi sun bi shi kuma sun harbe shi sau da yawa.[5]
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Yayi aure kuma ya haifi yara biyu. [6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "OSI Mourns the Loss of African AIDS Activist Omololu Falobi". www.opensocietyfoundations.org (in Turanci). Retrieved 2020-10-19.
- ↑ "The Omololu Falobi Award". AVAC (in Turanci). 2014-02-18. Retrieved 2020-10-19.
- ↑ "On World AIDS Day, we remember our Brother OMOLOLU FALOBI". Nigeria Health Watch (in Turanci). 2014-12-02. Retrieved 2020-10-19.
- ↑ "Omololu Falobi, Nigerian Journalist/HIV-AIDS Activist, 1971-2006 | Internews". internews.org. Archived from the original on 2017-07-08. Retrieved 2020-10-19.
- ↑ "Killed: Omololu Falobi, JAAIDS Founder and Executive Director | Chicago Afrobeat Project | Carrying the Torch Since 2002". Chicago Afrobeat Project (in Turanci). Retrieved 2020-10-19.
- ↑ "Pioneering AIDS Journalist Omololu Falobi Dies". POZ (in Turanci). 2006-10-09. Retrieved 2020-10-19.
Hanyoyin haɗin waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Ban kwana da Mai Rahadodi Mara tsoro Archived 2022-10-02 at the Wayback Machine 2006
- https://nigeria-aids.org/