Jump to content

Osman Nuhu Sharubutu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Osman Nuhu Sharubutu
Chief Imam of Ghana (en) Fassara

1993 -
Rayuwa
Haihuwa Accra, 23 ga Afirilu, 1919 (105 shekaru)
ƙasa Ghana
Karatu
Harsuna Turanci
Larabci
Hausa
Sana'a
Sana'a Liman, Ulama'u da philanthropist (en) Fassara
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulunci
hoton usman nuhu
hoton osmanu nuhu

Osmanu Nuhu Sharubutu malamin addinin Musulunci ne, Babban Limami a kasar Ghana, memba na Majalisar Zaman Lafiya ta Kasa kuma wanda ya kafa kamfanin SONSETFund da IPASEC.[1][2][3][4][5][6]

Osmanu Nuhu Sharubutu haifaffen Nuhu Sharubutu da Hajja A'ishatu Abbass a garin Accra Cow-lane an haifeshi ne a cikin watan Afrilu na shekara ta alif dari Tara da sha tara 1919.[7][8]

Osmanu ya fara karatunshi a gida daga mahaifinsa da rana sannan tare da mahaifiyarsa da daddare.[9] Osman mahaifinsa ne ya tura shi zuwa wani sabon yanayin ilmantarwa bayan ya ga sadaukarwa ga littattafai da ilmi. An dauke shi zuwa Kumasi kuma can ya zama wurin karatun sa. Abdullah Dan Tano ne ya karantar dashi. Ya shiga cikin Nahawun Larabci, Adabin Larabci da Rubutu, Fikihun Musulunci da Hadisai.[10]

Osman Nuhu Sharubutu

Bayan karatunsa a Kumasi, ya ba da lokacinsa wajen koyar da matasa musulmai masu son zama masu tunani da ilimi na Musulunci. Osman ya ci gaba da neman ilimi har ma a matsayinsa na malami kansa.[8]

A cikin shekara ta alif dari Tara da saba'in da hudu shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da hudu 1974, an nada Osman a matsayin Mataimakin Babban Limamin yankin na Ghana bayan tattaunawar tsakanin masana addinin Musulunci da sauransu.[8]

Nadin nasa anyi shi ne duba da irin kwazo da yake da shi wajen karantar da addinin Musulunci. Ya yi watsi da tayin da aka yi masa amma wasu shugabannin Musulmai suka tilasta shi ba shi tunani.[10]

Osman Nuhu Sharubutu

A shekara ta alif dari tara da casa'in da uku shekarar 1993, an nada shi Babban Limamin kasar Ghana na Al'ummomin Musulmai a kasar ta Ghana.[10]

  1. "Give us violent-free elections - Chief Imam urges EC". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.
  2. "National Chief Imam urges Muslims to adhere to ban on religious gathering during Ramadan". www.ghanaweb.com (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.
  3. Alhaji alhasan abdulai (abdulai.alhasan@gmail.com) (August 8, 2013). "Lets Emulate The Life of The Paragon of Virtue -Sheikh Dr Usman Nuhu Sharubutu National Chief Imam of Ghana". VibeGhana. Retrieved 20 January 2014.
  4. "Chief Imam Sheikh Osman Nuhu Sharubutu mourns Mills". SpyGhana. July 27, 2012. Archived from the original on 1 February 2014. Retrieved 20 January 2014.
  5. Muhammed Suraj Jawando (February 24, 2011). "PRESS RELEASE BY HIS EMINENCE THE NATIONAL CHIEF IMAM OF GAHNA, SHEIKH DR. OSMANU NUHU SHARUBUTU". ModernGhana. Retrieved 20 January 2014.
  6. Ghana News Agency (July 26, 2012). "Protect the principles of Islam – Sheikh Nuhu Sharubutu". GhanaWeb. Retrieved 20 January 2014.
  7. 122108447901948 (2019-06-04). "Biography of the National Chief Imam Sheikh Dr Osmanu Nuhu Sharubutu". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-01-11.CS1 maint: numeric names: authors list (link)
  8. 8.0 8.1 8.2 "Chief Imam turns 101 today". www.ghanaweb.com (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.
  9. 122108447901948 (2019-06-04). "Biography of the National Chief Imam Sheikh Dr Osmanu Nuhu Sharubutu". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-01-11.CS1 maint: numeric names: authors list (link)
  10. 10.0 10.1 10.2 "Chief Imam turns 101 today". www.ghanaweb.com (in Turanci). Retrieved 2020-05-26.