Jump to content

Patience Oghre Imobhio

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Patience Oghre Imobhio
Rayuwa
Cikakken suna Patience Oghre Imobhio
Haihuwa 20 century
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jos
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a darakta da jarumi
Imani
Addini Kiristanci
IMDb nm1968451

Patience Oghre Imobhio ƴar Najeriya ce kuma daraktar fina-finai da talabijin, haka-zalika ƴar wasan kwaikwayo. Ta kammala karatun digiri na biyu a Jami'ar Jos a fannin Theater Arts, ta shahara wajen shirya fina-finai irin su Dominos, Spider da Household, da shirye-shiryen TV irin su Dear Mother da Everyday People.[1][2] A shekarar 2015 Mujallar Pulse ta bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin "Daraktocin fina-finan Najeriya mata 9 da ya kamata ku sani" a masana'antar fina-finan Nollywood.[3]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta karanci Theatre Arts a Jami'ar Jos. [4] Ta auri Osezua Stephen-Imobhio.[5]

Ta fara aikin wasan kwaikwayo ne a shekarar 1995 amma ta yanke shawarar cewa ta fi sha'awar jagorantar fina-finai. Bayan ta kammala Jami’ar Jos ta koma Legas ta shiga harkar Zeb Ejiro. Imohbio ta shahara wajen bada umarni kamar a shirin fim da ta bayar da umarni da suka haɗa da; Dominos, Spider and Household, da shirye-shiryen TV kamar Dear Mother da Everyday People.[6]

  1. "Patience Oghre". IMDb.
  2. "Patience Oghre-Imobhio : Biography | Filmography | Awards - Flixanda". Archived from the original on 2022-03-17. Retrieved 2023-11-08.
  3. "9 Nigerian female movie directors you should know". Pulse. 5 October 2015. Archived from the original on 20 August 2017. Retrieved 20 September 2016.
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-11-08. Retrieved 2023-11-08.
  5. "My husband did not propose to me — Patience Oghre". 10 July 2016.
  6. "Patience Oghre Imobhio: My life behind the camera". 18 April 2020.