Jump to content

Rahmon Adedoyin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rahmon Adedoyin
Rayuwa
Haihuwa Ile Ife, 1 ga Janairu, 1957
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa 30 Mayu 2023
Ƴan uwa
Abokiyar zama Iyabo (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
All Saints University School of Medicine (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a Malami da ɗan kasuwa

Rahmon Adegoke Adedoyin, MD (an haife shi ne a ranar 1 ga watan Janairu shekarar 1957) ƙwararren ɗan Najeriya ne kuma ɗan kasuwa. Shi ne wanda ya kafa kuma ya mallaki Jami’ar Oduduwa Polytechnic, Ile-Ife.[1] A wata hira da jaridar Vanguard, Rahmon ya yi iƙirarin cewa marigayi Oba Okunade Sijuwade ya zaɓe shi a matsayin Ooni na Ife kafin rasuwarsa sabodanci gaban da ya samu, musamman a mahaifar Yarbawa".[2]

Rayuwar farko, ilimi da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Rahmon Adegoke a gidan sarautar Akui mai mulki a tsohon birnin Ife a jihar Osun,[3] inda ya kammala karatunsa na firamare da sakandare. Ya wuce Jami'ar Ife (yanzu Jami'ar Obafemi Awolowo) inda ya samu digiri na farko a fannin Kimiyya a shekarar 1983 bayan ya karanci Ilimin Lissafi. Ya kuma halarci Jami'ar Centurion International University, California inda ya sami digiri na biyu kuma ya ci gaba da yin digiri na uku a 1996 daga Makarantar Magunguna ta Jami'ar All Saints, New York City.[4]

A ƙoƙarin inganta ilimi a Najeriya, Rahmon ya kafa Polytechnic ɗin Ile-Ife a shekarar 1984 da Jami'ar Oduduwa a 2009. Shi ma'aikaci ne a Cibiyar Ƙididdigar Masana'antu ta Najeriya.[4]

Zargin kisan gilla

[gyara sashe | gyara masomin]

An kama Adedoyin ne a watan Nuwamban 2021 bayan mutuwar Adegoke Timothy a otal ɗin sa na Hilton wanda shi ne ya assasa.[5][6][7] An hana shi belinsa amma an ba shi damar zuwa wuraren kiwon lafiya da ya ke so a gaban kotu.[8]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-10-27. Retrieved 2023-03-12.
  2. https://www.vanguardngr.com/2015/08/ooni-nominated-me-as-his-succesor-before-he-died-adedoyin-2/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2015-09-11. Retrieved 2023-03-12.
  4. 4.0 4.1 https://www.notablenigerians.com/?p=4111[permanent dead link]
  5. https://saharareporters.com/2021/11/17/police-arrest-owner-oduduwa-university-connection-death-oau-mba-student
  6. https://saharareporters.com/2021/11/14/exclusive-osun-police-arrest-6-mba-student-%E2%80%98disappears%E2%80%99-after-lodging-hotel-oduduwa
  7. https://punchng.com/adedoyins-son-supervised-evacuation-burial-of-oau-student-flees-cp/
  8. https://punchng.com/oau-student-hotel-owner-denied-bail-granted-access-to-medical-services/