Rufa'i Garba
Rufa'i Garba | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Augusta, 1998 - Mayu 1999 ← Rasheed Adisa Raji - Attahiru Dalhatu Bafarawa →
21 ga Augusta, 1996 - 6 ga Augusta, 1998 ← Mike Attah - Emmanuel Ukaegbu → | |||||
Rayuwa | |||||
Cikakken suna | Rufai Garba | ||||
Haihuwa | 29 Mayu 1988 (36 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Karatu | |||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
A ranar 20 ga watan Afrilun shekara ta 1996, gwamnatin soja ta hambarar da Alhaji Ibrahim Dasuki, Sarkin Musulmi na 18 a Sokoto. A matsayinsa na Gwamnan Sakkwato a shekarar 1999, Rufai Garba ya amince da sasantawa da Dasuki kuma ya samar masa da tsarin walwala.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Kyaftin Rukuni (Sojan Sama) Rufa'i Garba ya kasance mai kula da harkokin mulkin soja na Jihar Anambra a kasar Nijeriya daga ranar 21 ga watan Disamban shekara ta alif 1996 zuwa 6 ga watan Agusta shekara ta alif 1998 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha, sannan na Jihar Sakkwato daga ranar 6 ga watan Agusta shekara ta alif 1998 zuwa 29 ga watan Mayu shekara ta alif 1999 a lokacin rikon kwarya Gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar, lokacin da ya mika wa zababben Gwamna Attahiru Dalhatu Bafarwa.[1]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]A matsayinsa na Gwamnan Anambra ya amince da gina ginin helkwatar hukumar Ilimi ta Jiha, amma ba a yi komai ba har aka fara aiki a shekarar 2009. A watan Fabrairun shekara ta 1998, gobarar abin da ba a bayyana ba ta kone ofishin gwamnan a gidan Gwamnatin Jihar Anambra. A watan Agusta shekara ta alif 1998 ya ce 'yan asalin jihar Anambara suna tsoron rundunar yaki da aikata laifuka kamar yadda suke tsoron masu laifi. Ykuma a ce rundunar tana karbar kudi a shingayen hanya tare da tsare mutane ba bisa ka’ida ba, kuma ya ce gwamnati za ta murkushe wannan aiki.[2]