Jump to content

Rundunar Haɗin Gwiwa Ta Farar Hula

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rundunar Haɗin Gwiwa Ta Farar Hula
Membobin CJTF.
yan aikin sa kai Maiduguri
Yan sa kai 2015

Rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force (CJTF) wani gungu ne na ‘yan bindiga da aka kafa a Maiduguri, jihar Borno, Najeriya domin taimakawa wajen fatattakar mayakan Boko Haram daga garinsu. Kungiyar ta mallaki muhimman makamai kuma tana da mambobin mata.[1][2] Kungiyar ‘yan banga tana da mayakan sa kai sama da 26,000 a arewa maso gabashin jihohin Borno da Yobe, wadanda 1,800 ne kawai ke karbar albashi ($ 50 a wata).[3] Rundunar ta CJTF ta yi asarar rayuka kusan 600 a rikicin, inda ta kirga duka ‘ya’yanta da suka rasa da kuma wadanda suka bata.[3]

Ana zargin CJTF da cin zarafi, da suka hada da yanka maza a gefen wani kabari, karkatar da abinci da aka tanada domin iyalan da ke fama da yunwa da dukan maza da kuma cin zarafin mata da 'yan mata a sansanonin.[3]

  1. "Civilian JTF women emerge in Borno - Search for female insurgents". Archived from the original on 11 December 2013. Retrieved 9 December 2013.
  2. "Women join civilian JTF in hunt for Boko Haram". Retrieved 9 December 2013.
  3. 3.0 3.1 3.2 "The volunteers who helped beat back Boko Haram are becoming a problem". The Economist. 1 October 2016. Retrieved 1 October 2016.