Jump to content

Safia Elhillo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Safia Elhillo
Rayuwa
Haihuwa Rockville (en) Fassara, 16 Disamba 1990 (34 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Sudan
Karatu
Makaranta Gallatin School of Individualized Study (en) Fassara
New School (en) Fassara
Sana'a
Sana'a maiwaƙe da marubuci
Kyaututtuka
safia-mafia.com…

 

Safia Elhillo (Larabci; an haife ta a ranar 16 ga watan Disamba, 1990) mawakiya ce 'yar kasar Sudan da Amurka wacce aka sani da rubuce-rubuce da wakokin baka. Elhillo ta sami digiri na BA daga Makarantar Gallatin a Jami'ar New York da kuma MFA a fannin shayari daga The New School. Elhillo ta yi wasanni a duk faɗin duniya. Ta samu yabo saboda aikinta kuma ta kasance wacce ta karɓi kyaututtuka masu daraja da yawa.[1] Elhillo ta yi wasa a dandali tare da sanannun mawaƙa kamar Sonia Sanchez kuma ta koyar a Split This Rock da Tin House Summer Workshop. [2] A halin yanzu ta kasance daliba ta Wallace Stegner[3] a Jami'ar Stanford .[4]

An haifi Elhillo a ranar 16 ga watan Disamba, 1990, a Rockville, Maryland, ga iyayen 'yan kasar Sudan.[5] Ta girma Musulmi.[6]

Wakokinta sun bayyana a wallafe-wallafe da dama, ciki har da mujallar Poetry, Callaloo, da kuma jerin shayari-na kwana bakwai na Academy of American Poets’,[7] da dai sauransu, da kuma cikin jerin shayarai irin su, The BreakBeat Poets: New American Poetry in the Age of Hip-Hop, Women of Resistance: Poems for a New Feminism, da kuma New Daughters of Africa.[8]

Elhillo ta yada ayyukanta a dandali ciki har da TEDxNewYork, Ba Kamar Kowacce Kamfe ba ta Under Armour, Gidan Wasan Kwaikwayo ta Kasar Afurka Kudu, Sabon Gidan Wasan Kwaikwayo ta Amsterdam, da kuma Verses & Flow na TV1's.

Kyaututtuka

[gyara sashe | gyara masomin]

An gabatar da Elhillo don lambar yabo ta Pushcart Prize, inda ta samu ambato na musamman a wajen kyautar Pushcart Prize na shekara ta 2016.[9] Tare da ita aka lashe lambar yabo ta Jami'ar Brunel don Shayarin Wakokin Afurka na shekara ta 2015, kuma ta lashe kyautar Sillerman Don Littafin Farko don Wakokin Afurka, kuma ta samu tallafin karatu da wuraren zama daga Cave Canem, The Conversation,[10] da kuma SPACE on Ryder Farm. Jerin wakokinta Yaran Junairu ya lashe kyautar Lambar Yabo ta Littattafan Larabawan Amurka, ya kuma karbi Kyautar George Ellenbogen na wakokin shayari, ta kasance 'marubuciya 'yar kasar Sudan da Amurka ta farko da ta lashe wannan kyauta.[11] the first Sudanese American author to win the award.[12] A cikin shekara ta 2018, an kuma lissafo ta a cikin jerin Forbes ta Africa na "30 kasa da 30", a rukunin masu fasaha.[13] Elhillo ta kuma lashe tallafin karatu na Ruth Lilly and Dorothy Sargent Rosenberg na shekara ta 2018, daga Gidauniyar Wakokin Shayari.[14]

Masu cikakken tsawo

  • The January Children (University of Nebraska Press, 2017).
  • Home Is Not A Country (Penguin Random House, 2021).
  • Girls That Never Die: Poems (Penguin Random House, 2022).
  • Bright Red Fruit (Penguin Random House, 2024).

Chapbooks

  • ars poetica (MIEL, 2016)
  • a suite for ol' dirty (MIEL, 2016)
  • Asmarani (Akashic Books, 2016)
  • The Life and Times of Susie Knuckles (Well & Often Press, 2012)

Jigo A cikin 'Ya'Yan Junairu, Elhillo ta zurfafa a cikin asali da iko, musamman akan batun 'yan kasa. A cikin Bright Red Fuit kuwa, Elhillo ta zurfafa akan asali da kuma begen soyayya ta hanyar amfani da duka rubutu da bayanai.[15]

  1. Elhillo, Safia, "Bio", Safia-Mafia website, 2017. Retrieved March 20, 2017.
  2. "Summer Workshop". Tin House (in Turanci). Retrieved 2024-06-14.
  3. "Meet the Stegner Fellows | Creative Writing Program". creativewriting.stanford.edu. Retrieved December 7, 2019.
  4. "Meet the Stegner Fellows | Creative Writing Program". creativewriting.stanford.edu. Retrieved December 7, 2019.
  5. "'Daughters full of all the wrong language'", Newsday, BBC World Service, July 9, 2015.
  6. Elhillo, Safia. "Good Muslim/Bad Muslim". Poetry Magazine. Poetry Foundation.
  7. Elhillo, Safia, "how to say" at poets.org.
  8. "Podcast #8: Safia Elhillo". Have Your Read … ?. September 23, 2019.
  9. "Awards & Recognition", One Throne Magazine.
  10. "Everything Lost Will Be Given a Name: SAFIA ELHILLO with Alex Dueben". The Brooklyn Rail. October 5, 2017. Retrieved December 16, 2017.
  11. "2018 Arab American Book Award Winners", Arab American National Museum.
  12. Edoro, Ainehi (November 12, 2018). "On Black and Arab Identities: Safia Elhillo's Arab American Book Awards Acceptance Speech". Brittle Paper.
  13. "Under 30 Creatives" Archived ga Yuli, 12, 2018 at the Wayback Machine, Forbes Africa, June 4, 2018.
  14. "Poetry Foundation Announces 2018 Ruth Lilly and Dorothy Sargent Rosenberg Poetry Fellowships", Poetry Foundation, August 28, 2018.
  15. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named https://www.kirkusreviews.com/book-reviews/safia-elhillo/bright-red-fruit/