Samiha Ayoub
Samiha Ayoub | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kairo, 8 ga Maris, 1932 (92 shekaru) |
ƙasa | Misra |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama |
Ahmed El-Nahass (en) Mahmoud Moursy (en) |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm0044066 |
Samiha Ayoub ( Larabci: سميحة أيوب ) 'yar wasan kwaikwayo ce ta ƙasar Masar wacce tayi fice a wasanninta na fage, a cikin fina-finai da kuma shirye shiryen talabijin. A cikin shekarar 2015, ta sami lambar yabo ta (Nile Award in the Arts),[1][2] kuma a cikin wannan shekarar dai, (the large hall in the National Theater) ya saka sunan ta don girmama irin rawar da kuma jarumar take takawa a sana'arta ta fitowa a cikin shirye-shiryen wasanni sinima da wasan kwaikwayo, da gudummawar da kuma take bayarwa a (theatrical arts) a lokacin wasan kwaikwayo a Masar.[3]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Samiha Ayoub a Shubra, Alkahira a shekara ta 1932.
Ta yi karatu a Makarantar Nun, sannan ta shiga Acting institute a shekarar 1952. Ci gabanta ya zo ne bayan rawar da ta taka a cikin fim ɗin "Samara" da kuma Rabaa ElAdawya wanda shirye-shirye ne masu dogon Zango na ƙafar sadarwa ta rediyo (radio series).
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Daga shekarar 1972 – 1975, Ayoub ta mallaki gidan wasan kwaikwayo na zamani, kuma daga 1975 – 1985, ta kasance shugabar gidan wasan kwaikwayo ta Al-Qawmy.
Ta yi wasan kwaikwayo a cikin shahararrun miniseries na talabijin El Miraya tare da Salah Zulfikar a shekarar 1984.[1][4]
Wasanni
[gyara sashe | gyara masomin]Fina-finai
[gyara sashe | gyara masomin]- Motashareda
- Shatea Al-Gharam Wal Wahsh
- Bein El Atlal (1959) [1]
- Tita Rahiba (2012) [1]
- El-Leila El-Kebira (2015) [1]
Talabijin
[gyara sashe | gyara masomin]- El Miraya (1984)
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Ta yi aure sau uku, ta auri jarumi Mohsen Sarhan, bayan nan ta auri jarumi Mahmoud Morsy, da kuma marubucin wasan kwaikwayo Sa'ed Eddine Wihbe (Saad Eddin Wehbe).[5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 "New book celebrates Egypt's famed actress Samiha Ayoub". Ahram Online. 6 March 2016. Retrieved 28 November 2018.
- ↑ "Samiha Ayoub, Nagy Shaker, Hassan Sharara among winners of top State Awards from arts". Ahram Online. 14 June 2015. Retrieved 28 November 2018.
- ↑ "Samiha Ayoub to be guest of 'Molhem' project". Egypt Today. 5 November 2017. Retrieved 28 November 2018.
- ↑ Series - المرايا - 1984 Cast، Video، Trailer، photos، Reviews، Showtimes (in Turanci), retrieved 2022-04-02
- ↑ "Samiha Ayoub Support's Cairo Festival Decision to Support Palestine". Al Bawaba. 15 November 2000. Retrieved 28 November 2018.