Jump to content

Samuel Okwaraji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Samuel Okwaraji
Rayuwa
Haihuwa Orlu (Nijeriya), 19 Mayu 1964
ƙasa Najeriya
Mutuwa Lagos, 12 ga Augusta, 1989
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Gazawar zuciya)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  GNK Dinamo Zagreb (en) Fassara1985-198610
FC Kärnten (en) Fassara1986-1987
  SSV Ulm 18461987-1988285
  VfB Stuttgart (en) Fassara1987-198900
  SSV Ulm 1846 Fußball (en) Fassara1987-1989
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya1988-198981
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Samuel Sochukwuma Okwaraji (an haife shi ranar 19 ga watan Mayu, 1964 - 12 ga watan Agusta, 1989) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ya bugawa Najeriya wasa. Ya kuma kasance ƙwararren lauya wanda ya yi digiri na biyu a fannin shari'a na duniya daga Jami'ar Pontifical Lateran ta Habasha. Ya yanke jiki ya faɗi nan take ya mutu sakamakon bugun zuciya a mintuna 77 na wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da ƙasar Angola a filin wasa na Legas da ke Surulere, jihar Legas a ranar 12 ga watan Agustan shekarar 1989.

Farkon rayuwa da aiki[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Okwaraji a ranar 19 ga watan Mayu shekarar 1964 a Orlu, Jihar Imo, Najeriya.

Okwaraji ya yi aiki a Turai wanda ya hada da bugawa AS Roma (1984 – 1985), NK Dinamo Zagreb (1985 – 1986), Austria Klagenfurt (1986 – 1987), VfB Stuttgart (1987 – 1989) da SSV Ulm 1846 (lamuni) 1987-1988) yayin da yake kammala karatunsa na shari'a. An yi wasan a ranar 30 ga watan Afrilu 1986, sannan Dinamo Zagreb yaci 12-0 Samuel yakan buga wasanni na musamman a Yankin Yugoslav na farko wasa daya ka sance Wasanni akan buga a siterdiyom a yankin Zagreb,a fannin zagaye na 29th Dinamo Zagreb ya ci 4:3.

Yana wasa tare da K. Berchem Sport na Belgium a lokacin mutuwarsa. [1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. The legend of fallen Super Eagles star Samuel Okwaraji – Part two: How he hit the limelight at Naija Super Fans, 28 September 2019, Retrieved 4 December 2020