Jump to content

Shaida Zarumey

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Shaida Zarumey
Rayuwa
Haihuwa Bamako, 1938 (86/87 shekaru)
ƙasa Nijar
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a marubuci, sociologist (en) Fassara da maiwaƙe
Employers Majalisar Ɗinkin Duniya

Fatouma Agnès Diaroumèye (am haifeta a shekarar 1938) ƙwararriyar mai ilimin zamantakewar jama'a ce kuma mawaƙiya ' ƴar Nijar, tana ɗaya daga cikin na farko a ƙasarta da ta fara rubuta Faransanci.

Diaroumèye, wacce aka haifa a Bamako ga mahaifinta ɗan Nijar da uwa ƴar ƙasar Mali,[1] Diaroumèye ta yi shekaru goma na farkon rayuwarta a Nijar, inda ta kammala karatunta na firamare. Ta ci gaba da karatunta a Mali kafin ta sami digiri na uku a Paris a 1970. Masaniyar tattalin arziƙi ta hanyar horarwa, ta fara aiki a Dakar a Institut Africain de Développement Économique et de Planification na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda aka yi mata aiki daga 1970 zuwa 1975; sai ta zama mai aiki mai sadaukar da haƙƙin mata.[2] Ta yi tafiye-tafiye da yawa don tallafawa aikinta.[1] A matsayinta na mawaƙiya, a ƙarƙashin sunan alƙalami Shaida Zarumey, ta buga Alternances pour le sultan a 1981.[3]