Tashar wutar lantarki ta Jebba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tashar wutar lantarki ta Jebba
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaKwara
Ƙaramar hukuma a NijeriyaMoro (Nijeriya)
Geographical location Nijar
Coordinates 9°08′08″N 4°47′16″E / 9.1356°N 4.7878°E / 9.1356; 4.7878
Map
Maximum capacity (en) Fassara 578.4 megawatt (en) Fassara

Tashar wutar lantarki ta Jebba tashar wutar lantarki ce da ke a Jebba, matatar wutar lantarki ce da ke ketaren Kogin Neja a jihar Neja, Najeriya. Tana da ƙarfin samar da wuta megawatt 578.4, ya isa ya bawa gidaje 364,000. An ba da izinin kafa ta a ranar 13 ga Afrilun shekarata 1985, ko da yake samar da makamashi na kasuwanci ya fara ne a shekarar 1983.[1]

Wuri[gyara sashe | gyara masomin]

Tashar wutar lantarki ta Jebba tana kusa da Dam ɗin kainji da kusan kilomita ɗari 100 kilometres (62 mi),ly 40 kilometres (25 mi). sai kuma kusan kilomita arba'in (40) zuwa Mokwa birni mafi kusa kenan a sentar[2]

Wannan kusan kilomita 256 kilometres (159 mi) ta hanyar, kudu maso yamma da Minna, babban birnin jihar Neja.[3] Tashar wutar tana zaune a gefen Kogin Neja a iyakar tsakanin jihar Neja da jihar Kwara, kusan kilomita 91.5 kilometres (57 mi), ta kan hanya, arewa maso gabashin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.[4] Dam din Jebba yana zaune a 71.917 metres (236 ft) a sama ma'anar matakin teku .

Ƙarin bayani[gyara sashe | gyara masomin]

Tashar wutar lantarki mallakin gwamnatin tarayya ce, wanda injina masu zuƙar ruwa wato (turbines) ko wane yana da kusan megawat 96.4 a matsakaicin megawat 578.4 wanda yake badawa (maximum installed output of 578.4 mega)a yarjejeniyar yadda za'a kula da kuma tafiya da tashar wutar lantarki yana a ƙarƙashin.(Mainstream Energy Solutions Limited) Kampani ne wanda ya dogara da kansa.

Kwaskwarima da gyara[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Janairun 2021, kamfanin Mainstream Energy ya zaɓi Andritz AG, wani kamfanin haɗin gwiwar injiniya na Switzerland, don gyara layin injin da yake aiki da kuma dawo da shi zuwa tashar wutar lantarki zuwa matsakaicin ƙarfinsa. Ayyuka masu amfani da lantarki sun hada da:

(a) maye gurbin injin mai karfin megawatts 96.4 (b) girka sabon janareta 103MVA (c) girka sabuwar taransfoma (d) girka sabuwar hanyar canza waje da (e) sauya kayan aiki, ciki harda kofar shiga.[5][6]

Gyara da kwaskwarimar ana sa ran kashe kimanin NGN13.68 biliyan (dalar Amurka miliyan 36 ko kuma fam miliyan 30) Ana sa ran aikin gyara zai kasance har zuwa farkon kwata na 2024.[5][6]

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. International Hydropower Association (December 2020). "Our Member Organizations: Mainstream Energy Solutions Limited: Brief overview of the Kainji and Jebba Hydroelectric Power Plants: Jebba Hydroelectric Plant". London, United Kingdom: International Hydropower Association. Retrieved 30 January 2021.
  2. Template:Google maps
  3. Template:Google maps
  4. Template:Google maps
  5. 5.0 5.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named 6R
  6. 6.0 6.1 Chika Izuora (28 January 2021). "Jebba Hydroelectric Power Plant To Gulp N13.68bn". Leadership Nigeria. Abuja. Retrieved 30 January 2021.