Tashe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Tashe
tashien a Hausawa

Tashe wata al'adar Hausawa ce wadda ake yin ta a bayan kowane kwana goman (10) farko na watan azumin Ramadan[1] kuma a kowace shekara a kasar Hausa.[2][3]

A hangen Ishak Idris, kalmar tashe ta samo asali ne daga Tashi ko Tasar wani daga bacci. Kenan kacokam ta kuma samo tushenta ne daga kokarin farkar da Musulmi masu azumi daga bacci domin yin sahur.[4] Matasa dai su ne ke yin tashe musamman ma waɗanda ba su kai shekaru sha biyar ba, da makamantansu

Wasan tashe kuma wata al'ada ce da ake yi a ƙasar Hausa a lokacin azumin watan Ramalana, inda matasa har ma da yara kan yi shiga kala-kala, suna kida da waka. Tashe hanya ce ta fadakarwa, ilmantarwa da kuma ankarar ko nusar da mutane game da wasu batutuwan da suka shafi rayuwa[5]. Sannan ana amfani da tashe wajen tashin mutane daga barci domin su yi sahur. Kuma a kan sallami masu tashe da kudi ko hatsi da dai sauransu.[2]

Haka kuma tashe hanya ce ta nishadantar da masu azumi don su manta da gajiyar da suke tare da ita.[6]

Misalan wasannin Zabe[gyara sashe | gyara masomin]

Ga wasu daga cikin misalan wasannin da ake gudanarwa a yayin tashe, da sunayensu: _ Mama Ta Yi Yaji.

_ 'Yar Iska Ta Ki Zaman Aure.

_ 'Dan Kadau-Kadau.

_ Mai Katsaniya.

_ 'Dan Marad'i Ya Sille.

_ Karo-ba-shawara.

_ Mairama Da Daudu.

_ 'Dan dukununu.

_ Macukule.

_ Tsoho Da Gemu.

_ Ka Yi Rawa Kai Malam[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]