Jump to content

Udoma Udo Udoma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Udoma Udo Udoma
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Shekarun haihuwa 26 ga Faburairu, 1954
Wurin haihuwa Akwa Ibom
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya, Minister of Budget and National Planning (en) Fassara da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ilimi a Jami'ar Oxford, King's College, Lagos (en) Fassara da St Catherine's College (en) Fassara
Affiliation string (en) Fassara Ministry of Budget and National Planning of Nigeria
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party
Participant in (en) Fassara World Economic Forum Annual Meeting 2019 (en) Fassara

Udoma Udoma tsohon ministan ƙasafin kuɗi da tsare-tsare na Najeriya[1] kuma ɗan marigayi Sir Egbert Udo Udoma. Shi ne kuma abokin kafa Udo Udoma & Belo Osagie - ɗaya daga cikin tsofaffi kuma manyan kamfanonin lauyoyi na kasuwanci a Najeriya. [1] Archived 2017-11-21 at the Wayback Machine

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Udoma ya halarci makarantar Corona, Ikoyi, Legas daga shekarar 1962 zuwa 1964 da Nakasoro Primary School, Kampala, Uganda daga shekarar 1964 zuwa 1965. Ya halarci Kwalejin King da ke Legas inda ya yi karatun sakandire daga shekarar 1966 zuwa 1972 sannan bayan matakinsa A ya wuce St. Catherine's College, Oxford, Ingila inda ya samu digiri na BA (Law) a shekara ta 1976 da BCL a fannin shari'a a shekara ta 1977. An kira shi zuwa ƙungiyar lauyoyin Najeriya a cikin shekarar 1978, bayan ya samu digiri na BL a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya.[2]

Aikin majalisar dattawa[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓe shi Sanata mai wakiltar Akwa-Ibom ta Kudu a jihar Akwa-Ibom ta Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu ta Najeriya, inda ya yi takara a jam'iyyar PDP. Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun 1999.[3] An sake zaɓen shi a cikin watan Afrilun 2003, ya sake tsayawa takara a jam’iyyar PDP.[4] Bayan ya hau kan kujerar majalisar dattijai a cikin watan Yunin shekarar 1999, an naɗa shi a kwamitocin kula da asusun jama'a, shari'a, banki da kuɗin shiga, Kimiyya & fasaha, Privatization da Drug & Narcotics (mataimakin shugaba).[5]

Ministan gwamnatin tarayya[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2015, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Udoma a matsayin ministan kasafin Kuɗi da tsare-tsare. Ya yi aiki a wannan aikin har zuwa cikin shekarar 2019.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://web.archive.org/web/20161013000012/http://www.nationalplanning.gov.ng/index.php/about-us/cabinet-ministers
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-04-09. Retrieved 2023-04-09.
  3. http://psephos.adam-carr.net/countries/n/nigeria/nigerialeg2.txt
  4. http://www.dawodu.com/senator.htm
  5. https://web.archive.org/web/20091118151316/http://www.nigeriacongress.org/assembly/committees1.htm