Jump to content

Umrah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentUmrah

Iri pilgrimage (en) Fassara de Musulunci
Wuri Makkah
Ƙasa Saudi Arebiya
Addini Musulunci
Pilgrims circumambulating the Kaaba, in Mecca (Hijazi region of Saudi Arabia) during the Hajj
umrah

ʿUmrah (da larabci عُمرَة) Ziyarar musulunci ce zuwa Makkah, Hijaz, Saudi Arebiya, wanda Musulmai keyi, kuma ana aikata shine akoda yaushe cikin shekara, akasin aikin Ḥajji (حَـجّ) wanda shi yake da lokacin aikata shi a kalandar watan musulunci. Da larabci, ‘Umrah na nufin "ziyara wurin da mutane suka cika." A Sharia, Umrah na nufin yin Ɗawafin Ka‘abah (كَـعْـبَـة, 'Cube'), da Sa'i tsakanin Safa da Marwah, dukkanin su bayan Ihrami (yanayin tsarki). Dole mutum yashiga Ihrami a lokacin tafiyarsa a ƙasa sannan kuma ya wuce Miqat kamar Zu 'l-Hulafa, Juhfa, Qarnu 'l-Manāzil, Yalamlam, Zāt-i-'Irq, Ibrahīm Mursīa, ko wani wurin a al-Hill. Saidai akwai damammaki dabandaban ga matafiya ta jirgin sama, wadanda dole su shiga Ihram a dai-dai sanda suka shiga cikin birnin Mecca. Akan kira umrah da 'karamin aikin hajji', aikin Hajj wanda shine babban kuma mafi muhimmanci, shi dole ne akan kowane Musulmi dake da ikon yi. Amma Umrah ba dole bane, saidai ana matuƙar so musulmi ya aikata shi a rayuwarsa.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]