Usman Yusuf
Usman Yusuf | |
---|---|
Rayuwa | |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Sana'a | |
Sana'a | pediatrician (en) |
Usman Yusuf, farfesa ne a fannin ilmin halittar jini watau da turanci ana kiran haka da Oncology, kuma tsohon dalibin Jami'ar Ahmadu Bello ne, kuma ya yi aikin likitanci a nahiyoyi uku kamar haka: Afirka, Turai da Arewacin Amurka, bayan karatun likitanci watau da turanci MBBS a alif na 1982.[1] An nada shi babban sakatare kuma shugaban babban jami’in hukumar inshorar lafiya ta kasa watau (NHIS) a watan Agustan shekarar 2016 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.[2][3][4][5]
Aikace-aikace
[gyara sashe | gyara masomin]Usman Yusuf ya kammala karatunsa na digiri a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1982, inda ya sami digiri na MBBS kuma ya yi aikin likitanci a nahiyoyin duniya uku Afirka, Turai da Arewacin Amurka, tun daga lokacin ya zama mai ba da shawara ga likitan yara kuma dan kungiya na Kwalejin Likitoci ta Yammacin Afirka a shekarar 1989 kuma ya sami gurbin karatu don samun digiri na biyu a likitancin maguna na yankuna masu zafin yanayi, tsafta a Jami'ar turai na Liverpool (UK) a 1988. Ya koma asibitin Fred Hutchinson Cancer Research Hospital Seattle Washington, a kasar Amurka, a matsayin mataimakin farfesa a 2000 zuwa 2003, ya koma Saint Jude Children Research Hospital a Memphis, Tennessee, a matsayin mataimakin farfesa a Sashen dasawa da ƙwayoyin cuta kuma ya kai matsayin cikakken farfesa a 2008.[1]
Tun lokacin da ya zama shugaban NHIS ya sha fuskantar dakatarwa da dama, inda ya ki amincewa da wasu daga cikinsu, a kan cewa gwamnatin tarayyar Najeriya za ta iya dakatar da shi. Tun da farko hukumar ta dakatar da shi Ministan lafiya na Najeriya a shekarar 2017 da hukumar NHIS a watan Oktoban 2018.[6] Usman a cikin wani faifan bidiyo da aka yi a shekarar 2017 ya koka da cewa idan NHIS kasuwanci ce su bayyana fatarar kudi kuma hukumar NHIS ta rufe kashi daya bisa dari na 'yan Najeriya tsawon shekaru 12. A halin yanzu dai majalisar dokokin Najeriya na gudanar da bincike kan sa bayan da Diri Douye ya gabatar da kudirin da ya shafi muhimman al'amuran kasa a ranar 23 ga Oktoba 2018.[7]
A yanzu haka yana hutu har zuwa shekarar 2019 kamar yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarce shi. Sanarwar ta fito ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun ofishin sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha yayin da ba ya nan, Mista Ben Omogo, daraktan gudanarwa a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya an tura shi ne domin kula da harkokin shirin. An tsige Farfesa Yusuf a matsayin babban sakataren hukumar ta NHIS inda aka maye gurbinsa da Farfesa Mohammed Sambo.[7][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 https://peoplepill.com/i/usman-yusuf
- ↑ This Day News, This Day News. "Buhari Appoints Heads of Health Institutions". Retrieved 29 December 2018.
- ↑ Abbas Jimoh & Akor Ojoma, Abbas Jimoh & Akor Ojoma. "Buhari appoints new heads of health agencies". Archived from the original on 30 December 2018. Retrieved 29 December 2018.
- ↑ Premium Times, Premium Times. "Buhari appoints new heads of health institutions". Retrieved 29 December 2018.
- ↑ Uche, Akolisa. "FG appoints Yusuf new NHIS boss". Retrieved 29 December 2018.
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/health/health-news/372745-how-sacked-nhis-boss-yusuf-responded-to-premium-times-enquiry-using-swear-languages.html
- ↑ 7.0 7.1 https://www.premiumtimesng.com/news/more-news/338540-profile-meet-mohammed-sambo-the-man-tapped-to-replace-usman-yusuf-as-nhis-boss.html?tztc=1
- ↑ https://www.vanguardngr.com/2022/01/why-usman-yusuf-should-have-his-day-in-court-soonest/