Wasan burtu
Appearance
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Wasan burtu ya kasance wani tsohon wasa ne da akeyi a kasar hausa wanda har iyau wasu sassa na yankuna arewacin Najeriya suna yin shi,kamar yankuna zariya,Kano,Katsina da dai sauransu.Mafi yawan Hausawan da aka haifa ko suka girma a birane basu san wannan wasan ba. Wasan burtu ba kowa ke yinshi ba face Maharba ko Mafarauta wanda suka Gaji harbi ko farauta.
Lokacin da ake wasan burtu
[gyara sashe | gyara masomin]Ana wasan burtu a lokuta kamar haka:
- Lokacin da maharbi ya samu aure (wato zaiyi aure) kamar ranar da akayi Baiko
- Lokaci da akayi wa maharbi haihuwa Musamman idan aka haifi ɗa namiji (wato magajin shi).
- Ranar da aka ɗaura mishi aure.
- Ranar da zai aurar da ɗiyas sa
- Ranar sunan ɗa da aka haifa.
da sauran su.