Yakin Damasak
| ||||
Iri |
faɗa rikici | |||
---|---|---|---|---|
Bangare na | Rikicin Boko Haram | |||
Kwanan watan | 9 – 17 ga Maris, 2015 | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Participant (en) |
Yakin Damasak ya faru ne a ranar 18 ga watan Maris shekara ta 2015 lokacin da sojojin Nijar da na Chadi suka kai wa 'yan Boko Haram hari a garin Damasak na Najeriya. An fatattaki ‘yan Boko Haram daga garin bayan kwashe kasa da kwana guda ana gwabza kazamin fada.[1] A ranar 24 ga watan Nuwamban 2014 ne kungiyar Boko Haram suka kwace iko da garin Damasak, kuma ikon na karkashinsu har zuwa karshen wannan yakin. A lokacin da aka kwato garin ya kasance ba kowa.[2] Farar hular da suka rage a cikin garin daga marasa lafiya sai tsofaffin da ba za su iya barin garin ba.[3] Bayan yakin sojojin Chadi sun kafa sansanoni a wajen garin sannan jiragen helikwafta na Chadi guda biyu sun iso da wasu kayayyaki.[4]
Bayan nan[gyara sashe | gyara masomin]
A ranar 20 ga watan Maris, kwanaki biyu bayan yakin, sojojin Nijar da na Chadi sun gano wani wakeken kabari da mutane fiye da 90 aciki a karkashin wata gada dake a wajen birnin.[5][6] Gawarwakin fararen hular sun ji raunika ta hanyar iska ta hamada, wanda ke nuni da cewa an yi kisan kiyashi ne a wani lokaci da ya wuce.[7]
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "Soldiers drove the terrorists out of Damasak in Borno state [PHOTOS]". Pulse Nigeria (in Turanci). 2015-03-20. Retrieved 2021-01-14.
- ↑ "Boko Haram was 'driven out' of the northeastern Nigerian town". www.aljazeera.com (in Turanci). Retrieved 2021-01-14.
- ↑ "'Mass graves' were discovered". France 24 (in Turanci). 2015-03-21. Retrieved 2021-01-14.
- ↑ "Troops from Chad. Niger freed the Nigerian town from Boko Haram | The Seattle Times". 2015-04-02. Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2021-01-14.
- ↑ Aminu Abubakar and Melissa Gray (21 March 2015). "Mass grave found in former Boko Haram-held town". CNN. Retrieved 2021-01-14.
- ↑ "Mass grave found in recaptured Nigerian town". www.aljazeera.com (in Turanci). Retrieved 2021-01-14.
- ↑ "Soldiers from Niger and Chad discover at least 70 victims of Boko Haram". Washington Post (in Turanci). ISSN 0190-8286. Retrieved 2021-01-14.