Damasak
Damasak | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Jihar Borno | |||
Ƙaramar hukuma a Nijeriya | Mobbar | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Damasak babban birni ne a ƙaramar hukumar Mobbar, cikin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya . Tana kusa da yankin kogin Yobe da Komadugu Gana, [1] kusa da kan iyaka da Nijar .
Hanyoyi biyu kanana sun isa Damasak. Daya daga kudu zuwa Gubio da Maiduguri, babban birnin jihar Borno, dayan kuma yayi dodar zuwa Kukawa da Baga .
A cikin 'yan shekarun nan, matsalar kwararowar hamada a arewacin Najeriya ta kasance matsala a garin Damasak. [2]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]A cewar masana, Kamkama Modu, wani Karde ne daga Bagirmi ya kafa garin . [3]
Damasak wani yanki ne mai ƙarfi ga wayewar Sao a ƙarni na 16, an kuma kewaye shi da shinge ganuwa mai kauri da tsawo. Idris Alooma ne ya ci garin da yaki a cikin shekarar 1570s ko 1580, kamar yadda Ibn Furtu ya rubuta (wanda ke nuna Sao a matsayin "Sao-Gafata"). [4] [5]
Wurin da Damasak yake yanzu ba tabbaci kan cewa a salin wurin ne. [6] Masanin tarihi Graham Connah ya ziyarci yankin a cikin shekarar 1965 tare da wasu gungun mazauna yankin sun ba da rahoton cewa yanzu yankin Damasak tana da kusan kilomita daya 1 daga asalin inda take (inda za'a iya samun motsi), wanda kuma suka bayar da rahoton cewa an watsar dashi a farkon karni na shekarun 1800s amma an kwashe kusan shekaru 100 ana mamaye dasu. [7]
Bajamuse mai bincike Heinrich Barth (1821-1865) ya ba da rahoto a cikin 1850s cewa har yanzu ana iya gano Damasak daga wani kogi da aka sanya wa garin sunan sa, amma a halin yanzu ana kiran wannan kogin da sunan "Fatoghana". Ya kuma bayar da rahoton cewa Edris, Sarkin Bornu daga 1353-77, ya mutu a Damasak bisa ga wasu dalilan. [8]
A watan Maris din 2015, an samu gawawwakin mutane 70 a wajen garin. An gano gawarwakin ne bayan ya Boko Haram sun kwace garin . A ranar 24 Maris 2015, mazauna garin sun ce Boko Haram sun kwashe mata da yara sama da 400 daga garin yayin da suke tserewa harin sojoji a farkon wani watan.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Mortimore, Michael. Adapting to Drought: Farmers, Famines, and Desertification in West Africa, p. 244 (1989)(note 3 notes that the Komadugu Gana joins the Yobe at Damasak)
- ↑ Murray, Senan (23 January 2007). Nigerian houses swallowed by sand, BBC News
- ↑ Lange, Dierk. A Sudanic Chronicle: The Borno Expeditions of Idris Alauma (1564-1576) According to the Account of Ahmad b. Furtu, p. 44, 120-21 (1987)
- ↑ Shillington, Kevin. Encyclopedia of African history, Volume 1, entry on Borno (Bornu), Sultanate of: Mai Idris Alooma (1571-1603), p. 271 (2005)
- ↑ Diouf, Sylviane. Fighting the Slave Trade: West African Strategies, p. 23-26 (Ohio University Press 2003)
- ↑ Rothmaler, Eva. Place names in Borno and Yobe States (Northern Nigeria), pp. 115, 216 (2007)
- ↑ Three Thousand Years in Africa, p. 200 (1981)
- ↑ Travels and discoveries in North and Central Africa, Vol. II, p. 585 (1857)