Yauri
|
| ||||
| Wuri | ||||
| ||||
| Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
| Jihohin Najeriya | Jahar Kebbi | |||
| Yawan mutane | ||||
| Faɗi | 100,564 (2006) | |||
| • Yawan mutane | 29.75 mazaunan/km² | |||
| Labarin ƙasa | ||||
| Yawan fili | 3,380 km² | |||
| Bayanan Tuntuɓa | ||||
| Kasancewa a yanki na lokaci | ||||
Yauri, karamar hukuma ce dake a Jihar Kebbi, Arewa maso yamman Nijeriya.[1]
Yauri na daya daga cikin jerin garuruwa da rafin neja (River Niger) ya ratso a ciki, wannan ya saka sana'ar Su yake daya daga cikin sana'o'i da ake gudanarwa a garin. Musamman kabilan salkawa wadanda su aka fi sani da kamun kifi. Yauri ta tara kabila da yaruka kala-kala, daga cikin su akwai gunga ( ko kuma gungawa), kambari, salkawa, da sauransu. Yauri nada cikin shekaru 600 (daga 1460s-2020) sarakuna 42 wanda sarki Dr. Muhammad Zayyanu Abdullahi CON, FNSM shine bisa karagar mulki. [2]
Demographics
[gyara sashe | gyara masomin]Kabilun da ke zaune a Yauri sun haɗa da Shangawa, Gungawa, Dukawa, Kamberi, Hausawa, Nupe, Yarbawa da kuma Kanuri. Sai dai, rinjayar da Hausawa suka samu a tsarin siyasa da zamantakewar Arewacin Najeriya ya sa wasu daga cikin manyan kabilun Yauri suka fara karɓar al'adun Hausawa, wanda hakan ya haifar da Hausancewar wasu daga cikinsu. A halin yanzu, Hausawa ne suka fi rinjaye a shugabancin Yauri.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Yauri Local Government". www.finelib.com. Retrieved 2023-08-25.
- ↑ "Mainstream Foundation:Yauri". www.mainstreamfoundation.org. Archived from the original on 2022-10-06. Retrieved 2023-09-17.
