Yima Sen
Yima Sen | |
---|---|
Yima Sen, a lokacin ralin Bring Back Our Girls a Washington DC, 2014 | |
Haihuwa |
Benue State, Nigeria | Fabrairu12, 1951
Mutuwa | Oktoba 6, 2020 | (shekaru 69)
Aiki |
|
Shahara akan | Campaign for Democracy, Northern Elders Forum, Bring Back Our Girls |
Yara | 3 |
John Yima Sen (an haife shi ranar 12 ga watan Fabrairu 1951 ya rasu ranar 6 ga watan Oktoba 2020), ya kasance ɗan asalin ƙabilar Tibi dan ƙasar Najeriya mai basira, sa'annan kuma ɗan gwagwarmayar siyasa. Ya shiga cikin ƙungiyoyin siyasa da suka ƙalubalanci mulkin kama-karya na Ibrahim Badamasi Babangida.[1] Ya kasance Sakatare Janar na Yaƙin Dimokuraɗiyya wacce ake mata laƙabi da (Campaign for Democracy) a tura
Yemi ya kasance, a lokacin Jamhuriyar Najeriya ta Biyu, mataimakin sadarwa ga Shugaban Majalisar Dattijai, Chuba Okadigbo. Waƙda daga bisani ya kasance mai ba da shawarwari na musamman kan harkokin siyasa ga Shugaba Shehu Shagari kuma ya yi aiki a matsayin Darakta na Bayanai a cikin gwamnatin Aper Aku.[2]
Haka zalika, ya zma mai bada shawara na musamman kan bincike, manufofi da takardu a Jamhuriyar Najeriya ta huɗu, ga mataimakin shugaban kƙsa, Atiku Abubakar [3]
Bai tsiya nan ba, ya kasance Sakatare-Janar na Middle Belt Forum kuma ya zama Darakta-Janar ta Gamayyar Tsofaffin Arewa. Haka zalika, ya kasance sanannen mutum a cikin tashin hankali don haƙƙin 'yan tsiraru waɗanda suka nemi ci gaban al'ummomi a yankin Middle Belt kuma ya shiga cikin ƙungiyoyi da yawa da ke da niyyar warware batutuwa a ƙoƙarin haifar da inganta zaman lafiya.[4]
Duk da haka, yayin mayar da martani ga damuwowi da ke cikin siyasar Najeriya a cikin 2018, misali hutun kiwon lafiya na Shugaba Muhammadu Buhari, majalisar zartarwa da kuma rikice-rikicen iko a jiharsa, wato jihar Benue, an naƙalto daga gare shi, "akwai alama Najeriya ba za ta iya yin hakan ba tare da fitowar juyin juya hali ba. Ƙasar ta kai matakin lalacewa wanda ba za a iya sarrafa shi ba tare da fitawar juyin mulki ba".[5]
Ya karanta ilimin Sadarwar na Jama'a a Jami'ar Legas, Jami'ar California, Los Angeles, Amurka, da Jami'ar Amsterdam dake Netherlands. A cikin aikinsa na sadarwa, ya taɓa kasance wa mai ba da shawarwari kan bayanai a Shirin Ci gaban Majalisar Dinkin Duniya dake Nairobi, Kenya kuma ya zamo mai ba da shawarar
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Challenges and Prospects of Nigeria's Development at 50" (PDF). 2010.
- ↑ "Northern Elders' Forum DG, Yima Sen, is dead". premiumtimesng.com. 2020. Retrieved 9 November 2020.
- ↑ "Tribute to Yima Sen". dailytrust.com. 12 October 2020.
- ↑ "Yima Sen was an intellectual colossus – MBF". blueprint.ng. 2020. Retrieved 9 November 2020.
- ↑ "Nigeria Cannot Make It Without Revolutionary Exit Now – Dr Yima Sen". intervention.ng. 2018. Retrieved 9 November 2020.