Zaben Jahar Zamfara na 2015
Iri | gubernatorial election (en) |
---|---|
Kwanan watan | 11 ga Afirilu, 2015 |
Ƙasa | Najeriya |
Zaben gwamnan jihar Zamfara na 2015 shi ne zaben gwamnan jihar Zamfara karo na 5 . Wanda aka gudanar a ranar 11 ga Afrilu, 2015, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Abdul’aziz Abubakar Yari ya lashe zaben, inda ya doke Mamuda Aliyu Shinkafi na jam’iyyar People’s Democratic Party . [1]
APC na fidda gwani
[gyara sashe | gyara masomin]Dan takarar jam’iyyar APC, Abdul’aziz Abubakar Yari ne ya lashe tikitin tsayawa takara na jam’iyyar. An gudanar da zaben fidda gwani na APC a shekarar 2014. [2]
Zaben fidda gani na Jam'iyyar PDP
[gyara sashe | gyara masomin]Dan takarar jam’iyyar PDP, Mamuda Aliyu Shinkafi ne ya lashe tikitin tsayawa takara na jam’iyyar. An gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a shekarar 2014.
Sakamakon Zaben
[gyara sashe | gyara masomin]‘Yan takara 20 ne suka fafata a zaben. Abdul'aziz Abubakar Yari na jam'iyyar All Progressives Congress ne ya lashe zaben da kuri'u 716,964 Mamuda Aliyu Shinkafi na jam'iyyar PDP . yasamu kuri'u 201,938