Jump to content

Zaben gwamnonin Najeriya 2023

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentZaben gwamnonin Najeriya 2023
Iri gubernatorial election (en) Fassara
Kwanan watan 25 ga Janairu, 2024
Ƙasa Najeriya

An gudanar da zaben gwamnonin Najeriya na 2023 na gwamnonin jihohi a jihohi 31 cikin 36 na Najeriya. A ranar 18 ga watan Maris,a daidai lokacin da aka gudanar da zaɓen kowace Majalisar Dokoki ta Jiha, makonni uku bayan zaben shugaban kasa da na ƴan majalisar dokoki - yayin da za a gudanar da zaɓen jihar Imo, da Kogi da Bayelsa a ranar 11 ga watan Nuwamba.[1][2][3][4] Zaɓen gwamnonin da aka saba yi na ƙarshe na dukkan jihohin kasar shi ne a shekarar 2019 . Dukkanin Jihohin dai na da wa’adi biyu na Gwamnoni wanda hakan ya sa gwamnoni 18 da ke kan karagar mulki ba za su iya sake tsayawa takara ba.

Kafin zaɓen dai akwai gwamnonin APC 21, gwamnoni 14 na PDP, da na APGA guda ɗaya. Daga cikin ofisoshin gwamnan da za a yi zaɓe a shekarar 2023, 19 na ɗan jam’iyyar APC ne, yayin da 12 kuma ɗan PDP ne ke riƙe da shi.

  1. Oyekanmi, Rotimi (26 February 2022). "It's Official: 2023 Presidential, National Assembly Elections to Hold Feb 25 ". INEC News. Retrieved 27 February 2022.
  2. Jimoh, Abbas (26 February 2022). "INEC Sets New Dates For 2023 General Elections". Daily Trust. Retrieved 26 February 2022.
  3. "INEC shifts governorship, assembly polls by one week". The Punch. Retrieved 9 March 2023.
  4. Adenekan, Samson. "INEC releases date for Bayelsa, Imo, Kogi off-cycle governorship elections". Premium Times. Retrieved 25 October 2022.