Jump to content

Zainab Ibrahim Kuchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zainab Ibrahim Kuchi
Minister of State for Niger Delta Affairs (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1958 (65/66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Hajiya Zainab Ibrahim Kuchi An naɗa ta a matsayin ƙaramar ministar wutar lantarki ta kasar Najeriya da tsohuwar ministar harkokin Neja Delta daga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan . An nada ta a watan Yulin shekara ta 2011. Ita ma yar kasuwa ce wadda ta kirkiro kuma Shugaba na Kamfanin Daralkuchi.[1]

Zainab kuma lauya ce kuma 'yar kasuwa mai sama da shekaru talatin da biyar 35 na kwarewa a fannin shari'a da gudanarwa. Ta fara ne a shekara ta 1981, inda ta yi aiki tare da hedkwatar shari’ar jihar Neja. Bayan ta kammala yin NYSC, an ci gaba da aiki da Ma'aikatar Shari'a Minna kuma ta yi aiki a can kimanin shekaru takwas da rabi. Zainab ta yi aiki a Babban Bankin Najeriya daga watan Mayu shekara ta 1989 zuwa watan Disambar shekara ta 2004 lokacin da ta yi ritaya don kafa kamfanin ta na ba da shawara kan harkokin shari'a. Ita ce kuma ta kafa kuma Shugaba na Kamfanin Daralkuchi.

Sana'ar Siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya nada ta minista a majalisar ministocin ta don wakiltar jihar Neja. An kuma nada ta a matsayin karamar ministar wutar lantarki. A cikin watan Nuwamban shekarar 2011, ta sanar da sanya hannu kan yarjejeniya tare da Kamfanin Sinohydro . Kamfanin mallakin kasar China ne zai gina kamfanin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050 a Mambilla, Plateau a jihar Taraba . 30 ga watan Oktoban shekarata 2012, bayan taron Majalisar Zartarwa na Tarayya (FEC), Shugaba Jonathan ya umurce ta da ta sauya mukaminta da tsohuwar karamar ministar harkokin Neja Delta, Dairus Ishaku . Shugaba Jonathan ya ce karamin garambawul da aka yi wa majalisar ministocin shi ne karfafa bangarorin domin cimma burin 'yan Najeriya.

A shekarar 2014, an nada ta a matsayin mai kula da yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan na jihar Neja.

A ranar 11 ga watan Satumbar,shekarar 2013, an kori Zainab daga mukamin ministar wutan lantarki yayin wani taron FEC tare da wasu ministocin takwas.