Zainab Usman Sa'idu Ɗakin Gari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zainab Usman Sa'idu Ɗakin Gari
Rayuwa
Haihuwa 1979 (44/45 shekaru)
Sana'a

Zainab Usman Sa'idu Ɗakin Gari ( Zainab Umaru Musa Ƴar'adua ) an haife ta ranar 1 ga watan Oktoba shekarar 1979, a Katsina, Najeriya. Ita ɗiya ce ga tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Umaru Musa Yar'Adua kuma matar tsohon gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Usman Sa'idu Nasamu Ɗakin gari.[1][2][3][4]

Farkon Rayuwa da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An kuma haifi Zainab a jihar Katsina a ranar 1 ga watan Oktoba, shekarar 1979. Ta fara neman ilimi ne a makarantar Firamare dake Katsina tsakanin shekarar 1986 zuwa 1992. Ta fara karatun sakandire ne a makarantarGovernment Girls Secondary School Bakori local Government tsakanin shekarar 1993 zuwa shekarar 1996, sannan ta kuma koma Essence International School Kaduna tsakanin shekarar 1996 zuwa 1999. Ta kasance ɗaliba a Jami’ar Maiduguri, Jihar Borno, daga shekara ta 2000 zuwa 2002. Tsakanin shekarar 2003 zuwa 2006, ta kasance ɗaliba a Jami'ar Huron, dake a London, United Kingdom sannan kuma Kwalejin Gudanar da Ayyuka.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kuma kasance Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2015 sannan kuma ita ce wadda ta kirkira ZadaF Foundation for Women and Children Enpowerment.

Kyautuka/Girmamawa[gyara sashe | gyara masomin]

  • CibiyarFederal Medical Center, Birnin Kebbi Child Health Week, Equity 2009 (5 August 2009)
  • Gidauniyar Women for Peace International Global Peace Diplomat (30 September 2009)

Littafan da ta wallafa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Kabir, Hajara Muhammad. Ci gaban matan Arewa . [Nijeriya].  . Saukewa: OCLC890820657.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Kabir, Hajara Muhammad (2010). Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
  2. "Usman Saidu Nasamu Dakingari biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2022-05-16.
  3. siteadmin (2009-06-22). "Yar'adua's Family of Greed- A Photo Essay Of A Humble Beginning And Then A Super Luxurious Life". Sahara Reporters. Retrieved 2022-05-16.
  4. "Alleged Corruption: EFCC moves against Saraki's wife, Yar'Adua's daughter | Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2015-07-22. Retrieved 2022-05-16.