Jump to content

Zara Moussa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zara Moussa
Rayuwa
Haihuwa Niamey, 1980 (43/44 shekaru)
ƙasa Nijar
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a mawaƙi da rapper (en) Fassara
Sunan mahaifi Zara Moussa
Kayan kida murya

Zara Moussa (an haife ta a shekarar alif dari tara da tamanin miladiyya 1980) mawakiyar salon gambarar zamani ce yar kasar Nijar wadda akafi saninta da ZM.

Haifaffiyar birnin Niamey, Moussa ta fara tashe ne a shekarar 2002 lokacin da taci kyautar hip-hop contest a birnin na haihuwar ta.[1] kyautar da ofishin jaladancin Faransa ya dauki nauyi.[2] Zara itace sananniyar mace mawakiyar gambarar zamani (wato Hip Hop) a Yammacin Afrika gabadaya da ta fara fitar da kundi (album) wanda tasakama suna Kirari. Wakokinta sunfi dangantuwa ne akan harkokin yau da kullum, siyasa da kare hakkin mata,[1] da kima harkokin lafiya. Salon Zara na kama da salon mawakiyar Nijar dinnan Safiath [3]. Yawancin wakokin ta cikin harshen Faransanci tayi su, amma akwai wadanda tayi su cikin harsunan Hausa da Zarma.[4] Salon ta yazo da wani sabon babi tsakanin mawakan hip-hop na nahiyar Afrika.[5] Moussa tayi aure, kuma ta baiyana maigidanta wanda shike rubuta akasarin wakokinta da babban jarumi kuma mataimakinta wajen habbaka harkokin wakokin ta. Musamman ma a kasar da ake kallon waka da aibi, kuma ma kasar da maza ne kadai suka mamaye harkokin wakokin na Hip Hop.[2]

Waka Mintoci
Tout Va De Travers 3:54
Ma Rage 3:03
Kirari 3:29
Soyeya 3:26
Femme Object 3:45
Femme rurale 3:45
Ma Gate 3:17
Violence 4:18
Rapo 3:49
Prends Le Mic 3:28
Je Dois Patir

[6]

  1. 1.0 1.1 Alison Behnke (15 December 2007). Niger in Pictures. Twenty-First Century Books. pp. 70–. ISBN 978-0-8225-7147-6.
  2. 2.0 2.1 "Verdensmusikbanken - Verdensmusik i undervisningen - Interview med Zara Moussa". www.verdensmusikbanken.dk. Archived from the original on 4 March 2017. Retrieved 5 November 2017.
  3. Burgess, Sarah (11 December 2013). "Four Nigerien Women Musicians You Should Know: ZM (Zara Moussa)". Africa is a Country. Retrieved 5 November 2017.
  4. "Zara Moussa | Studio le Rocher". Studiolerocher.fr. Retrieved 5 November 2017.
  5. "Zara Moussa - virtualWOMEX". www.womex.com. Retrieved 5 November 2017.
  6. https://www.discogs.com/Zara-Moussa-Zara-Moussa/release/14496272