2Baba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg 2Baba
2face Idibia.png
Rayuwa
Cikakken suna Innocent Ujah Idibia
Haihuwa Jos, 18 Satumba 1976 (44 shekaru)
ƙasa Najeriya
Yan'uwa
Abokiyar zama Annie Macaulay–Idibia
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mawaƙi, mai rubuta waka da mawaƙi
Kayan kida voice (en) Fassara
IMDb nm1939824
2faceonline.com

Innocent Ujah Idibia (an haife shi a garin Shomolu, a Jihar Lagos, dake kudanci Nijeriya), Anfi saninsa da 2Baba, mawakin Dan Nijeriya ne, marubucin wakoki, mai samarda waka, kuma mai kirkiran sana'a. Kafin zuwa watan Yulin shekarar 2014, ana kiransa da suna 2face Idibia.[1] Yana daya daga cikin shahararrun mawaka a Nijeriya kuma daya daga cikin wadanda sukafi kyaututtuka a nahiyar Afirka, har wayau yana daya daga cikin masu kudin mawaka a Afirka.[2]

2Baba yasamu kyautar guda daya MTV Europe Music Award, da World Music Award, da kyautukan Headies guda biyar (Hip-hop award), da Channel O Music Video Awards guda hudu da kuma BET award daya akan ayyukan wakokinsa, yasamu MTV Africa Music Awards guda hudu, MOBO award guda daya, KORA award guda daya itama, da dai sauran wasu tarin kyaututtuka da tantancewa a ciki da wajen Nijeriya.'[3]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Njoku, Benjamin (27 July 2014). "2face changes name to 'Tu-baba'". Vanguard. Retrieved 30 July 2014.
  2. "Know Your Naija: 10 Nigerian Stars To Watch". MTV Iggy.
  3. "2baba". 2021-02-27.