Jump to content

Abdulkadir Rahis

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulkadir Rahis
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Maiduguri (Metropolitan)
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

ga Yuni, 2015 -
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

Rayuwa
Haihuwa Maiduguri (en) Fassara, 30 ga Yuni, 1968 (56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Abdulkadir Rahis (an haife shi a ranar 30 ga watan Yuni 1968) [1] ɗan siyasan Najeriya ne a halin yanzu yana aiki a matsayin ɗan majalisar wakilai ta Najeriya mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Maiduguri (Birnin) a majalisar wakilai ta ƙasa ta 10. Ɗan jam’iyyar APC ne kuma ya yi wa’adi uku a majalisar wakilai. [2]

Tarihi da farkon rayuwarsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Abdukadir ya yi karatu a kwalejin kimiyya da fasaha ta ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno, kuma ya kammala a shekarar 1989.[3]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Rahis ya fara harkar siyasa ne a shekarar 1990, lokacin da ya tsaya takarar kansila a shiyyar Shehuri ta Kudu da ke Maiduguri Metropolitan Council. A shekarar 1997 aka zaɓe shi shugaban Ward a ƙarƙashin jam'iyyar United Nigeria Democratic Party sannan a shekarar 1999 ya zama ma'ajin jam'iyyar All People's Party a Maiduguri Metropolitan Council.[3]

A cikin shekara ta 2001, an naɗa shi a matsayin Kansilan Kula da Ayyuka a Majalisar Dokokin Maiduguri, aikin da ya yi har zuwa shekara ta 2003. A shekarar 2003, an naɗa shi mamba a kungiyar kwallon kafa ta El-Kanemi Warriors, sannan ya zama shugaban hukumar. Ya kuma riƙe muƙamin shugaban matasan jihar Borno daga shekarun 2006 zuwa 2011 kafin Gwamna Kashim Shettima ya naɗa shi mataimaki na musamman. A cikin shekara ta 2012, an naɗa shi a matsayin Shugaban Kwamitin Riƙo na Maiduguri Metropolitan Council kuma ya yi aiki har zuwa shekara ta 2015.[3]

A shekarar 2015, an zaɓe shi a matsayin mamba mai wakiltar Maiduguri Metropolitan Federal Constituency na jihar Borno a majalisar wakilai, a ƙarƙashin jam'iyyar APC.[4]

  1. "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 9 December 2024.
  2. "10th National Assembly Members". Orderpaper.ng. Retrieved 9 December 2024.
  3. 3.0 3.1 3.2 Maitela, Muhammad. "Hon. Abdulkadir Rahis is committed to representing the community well". Hausa leadership.ng.
  4. Hussaini, Hayatu (January 5, 2021). "Hon. Abdulkadir Rahis: Borno lawmaker with a difference". Blueprint Newspapers Limited.