Jump to content

Abdullahi Abubakar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdullahi Abubakar
Rayuwa
Haihuwa 1 ga Janairu, 1936 (89 shekaru)
Sana'a

Imam Abdullahi Abubakar malamin addinin musulunci ne kuma mai taimakon jama'a. Ya shahara wajen ceto rayukan mutane 262 wadanda ba musulmi ba a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa al’ummarsa hari . [1] [2] [3]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Iman Abdullahi Abubakar a shekarar alif dari tara talatin da shida miladiyya 1936 a garin Bauchi dake jihar Bauchi a Najeriya. [4]

Imam Abubakar shi ne babban limamin masallacin Akwatti da ke garin Nghar, al’ummar karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato . A shekarar 2018, an kai hari a kauyukan Yelwan Gindi Akwati, Swei da Nghar inda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kashe mutane 80. [5] [6]

Limamin ya samu nasarar ceto rayukan mutane 262 wadanda galibi Kiristoci ne daga kabilar Birom ta hanyar boye su a cikin masallacin sa ta yadda ya hana maharan kashe su. [5]

A watan Yulin 2019, Imam Abdullahi Abubakar ya karbi lambar yabo ta ‘Yancin Addini ta Duniya daga Gwamnatin Amurka, wacce ta baiwa masu goyon bayan ‘yancin addini, tare da wasu shugabannin addini hudu daga kasashen Sudan, Iraq, Brazil, da Cyprus. [7] [6]

A watan Agustan 2019 ne shugaba Buhari ya ba da izinin shigar da Imam Abdullahi Abubakar cikin kwamitin malamai na kasa kuma yana cikin kwamitin mutane 80 da aka dorawa alhakin wayar da kan alhazan Najeriya a Mina yayin aikin Hajjin 2019.

Kyaututtuka

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. "Abdullahi Abubakar: Befitting honour to a prophet at home". TheCable (in Turanci). 2022-10-12. Retrieved 2022-10-21.
  2. "Nigeria: How Village Imam, Abubakar, Put His Life on The Line to Save Others In Barkin Ladi Attacks | The MacMillan Center Religious Freedom and Society in Africa". religiousfreedom.yale.edu. Retrieved 2022-10-21.
  3. "America honour Nigeria imam wey save Christians from killer 'herdsmen'". BBC News Pidgin. 2019-07-18. Retrieved 2022-10-21.
  4. Egbas, Jude (2019-08-09). "Muslim who saved 262 Christians from killer herdsmen explains why". Pulse Nigeria. Retrieved 2022-10-21.
  5. 5.0 5.1 5.2 Okogba, Emmanuel (2019-07-26). "A deserved honour for Imam Abdullahi". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2022-10-21. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  6. 6.0 6.1 "Muslim cleric who hid Christians during attacks honored in the US". CNN (in Turanci). 18 July 2019. Retrieved 2022-10-21. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":2" defined multiple times with different content
  7. 7.0 7.1 "CAN honours Plateau Imam who saved Christians from attacks | Dailytrust". dailytrust.com. 26 September 2021. Retrieved 2022-10-21. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content