Jump to content

Abubakar M. Gana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abubakar M. Gana
Rayuwa
Haihuwa Nasarawa, 25 Disamba 1987 (36 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Bayero
Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Jihar Nasarawa
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa

Abubakar M. Gana shi ne daraktan hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) a Najeriya. NECO wata hukuma ce ta gwamnati da ke da alhakin gudanarwa da kula da jarabawar ƙasa da ƙasa a Najeriya daban-daban da suka haɗa da jarrabawar kammala sakandare (SSSCE) da jarrabawar gama gari ta ƙasa (NCEE).[1][2]

An naɗa Gana a matsayin daraktan NECO a shekarar 2019. Kafin wannan, ya taɓa zama mataimakin daraktan NECO, da kuma daraktan ayyuka da tsare-tsare.[3]

A lokacin da yake riƙe da muƙamin daraktan NECO, Gana ya inganta gami da gyare-gyare da dama a harkar jarabawar. Waɗannan sun haɗa da ɓullo da tsarin ɗaukar hoton yatsa na biometric don hana magudi,[4] faɗaɗa ayyukan NECO ta yanar gizo, da ɓullo da sabon tsarin tantance ma'aikata. Ya kuma yi kokarin inganta jarabawar NECO da kuma ƙara nuna gaskiya da riƙon amana a ƙungiyar.

Ya yi digirinsa na farko a fannin Science in Psychology a Jami’ar Jihar Nasarawa, haka nan kuma ya yi Digiri na biyu a fannin Shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 2013, sannan kuma yana da Diploma na Post Graduate Diploma, M.Ed. da kuma PhD a fannin Guidance and Counseling daga Jami'ar Bayero Kano.[5][6][7]

  1. "Abubakar Gana | Ahmadu Bello University, Nigeria - Academia.edu". abu.academia.edu. Retrieved 2022-12-29.
  2. Okoli, Al Chukwuma; Abubakar, Mamuda (2021-11-01). "'Crimelordism': Understanding a New Phenomenon in Armed Banditry in Nigeria". Journal of Asian and African Studies (in Turanci). 56 (7): 1724–1737. doi:10.1177/0021909621990856. ISSN 0021-9096. S2CID 234364143 Check |s2cid= value (help).
  3. Adejo, Daniel (27 August 2019). "NECO releases May/June 2019 SSCE result". Radio Nigeria. Archived from the original on 14 September 2019.
  4. Hersey, | Frank (2019-06-07). "Digital ID in Africa this week: biometric pay delays and World Bank support | Biometric Update". www.biometricupdate.com (in Turanci). Retrieved 2022-12-29.
  5. "Meeting NECO'S Mandate Under The First Leadership Of Pioneer Staff, Abubakar M. Gana; Prospects, Challenges And Successes – Education Monitor News". Education monitor. 2019-12-21. Archived from the original on 2021-06-25. Retrieved 2022-12-29.
  6. "My NECO Exams". Archived from the original on 2023-01-27. Retrieved 2023-09-28.
  7. "NECO Acting Registrar Mr Abubakar Gana Archives – FRCN". Radio Nigeria. 2019-08-27. Archived from the original on 2021-06-19. Retrieved 2022-12-29.