Adam Disina

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adam Disina
Rayuwa
Haihuwa 1978 (45/46 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai da'awa

An haifi Sheik Ibrahim Adam Disina a shekara ta 1978 a garin Disina na karamar hukumar Shira a jihar Bauchi. Sheikh Ibrahim Adam Disina na daga cikin manyan malaman addinin Musulunci da ke jihar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya.

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Sheik Disina ya fara karatun allo da na firamare a garin Disina. Daga nan kuma ya tafi garin Bauchi domin ci gaba da karatun sakandare. Kuma daga nan ne ya fara katarun addinin ka'in da na'in.

Bayan kammala karatun sakandare ya tafi kwalejin ilimi ta garin Misau inda ya yi difloma. Sannan ya samu damar tafiya zuwa Jami'ar Musulunci ta Madina inda ya yi digiri na farko a fannin Hadisi.

Ya yi digiri na biyu a Jami'ar Jos, sannan ya yi digiri na uku a Jami'ar Usman Dan Fadiyo da ke Sokoto.

Malaman Sheik Disina[gyara sashe | gyara masomin]

Dakta Ibrahim Disina ya baiyana cewa ya tasirantu da malamai da dama a ciki da wajen Najeriya, wadanda suka ba shi gudunmowa a harkar neman ilimi.

Cikin malaman akwai Limamin garin Dushin Malam Yuguda a garin Disina, da Malam Ahmad Usman da Malam Salisu Zakariyya da Malam Ahmad Tijjani.

A ƙasar Saudiyya ma, Sheikh Disina ya ce ya fa'idantu da malamai da dama, musamman a Jami'ar Musulunci ta Madina.

Gwanayen Sheik Disina[gyara sashe | gyara masomin]

Sheikh Ibrahim Disina ya ce akwai wasu malamai a Najeriya da yake dauka a matsayin taurari, kuma suka zame masa gwaraza.

Daga cikinsu akwai Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam, wanda ya ce ya yi matukar tasiri a rayuwarsa ta ilimi.

Malam Disina ya ce ya ja wa Sheikh Jaafar baki har ya sauke wasu litattafai guda bakwai a garin Bauchi.

Haka kuma Malam Disina ya ce yana fata ya samu ɗumbin ilimi da bincike irin na Dakta Muhammad Sani Rijiyar Lemo.

A bangaren wayewa da dattako da faran-faran da jama'a kuwa, ya ce yana fata zama kamar Dakta Bashir Aliyu Umar.

A fannin iya mu'amala da jama'a da hukumomi kuwa yana fata ya zama kamar Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu.

Idan kuwa a jajircewa ne da gwagwarmaya da baiwar rubutu ne, Dakta Disina ya ce yana fata ya zama kamar Farfesa Mansur Sokoto.

Sana'o'in Sheik Disina[gyara sashe | gyara masomin]

Sheikh Disina ya ce ya yi sana'o'i da dama a kuruciyarsa, wasu saboda kiriniya irin ta yara, wasu kuma domin ya samu damar daukar nauyin karatunsa.

Daga cikin sana'o'in da malamin ya ce ya yi akwai dako da aikin lambu, da kamun kifi.

Ya ce daya daga abin da ba zai manta da shi ba a kuruciya akwai yaron mota, wato kwandasta. Ya yi wannan sana'ar ne a Kano inda yake bin mota tsakanin Sheka - Rimi - Asibiti.

Amma a yanzu, Dakta Ibrahim Disina babban manomi ne a jihar Bauchi, inda yake hada noma da kiwon dabbobi har ma da kiwon kifi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56531267
  2. https://hausa.legit.ng/mutane/1439875-sheikh-disina-abin-da-ya-sa-na-daina-yin-bikin-mauludi-bayan-na-tashi-mu-na-yi-a-da/