Jump to content

Adenike Osofisan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Adenike Osofisan
Rayuwa
Haihuwa Osogbo, 11 ga Maris, 1950 (74 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar Obafemi Awolowo
Georgia Tech (en) Fassara
Jami'ar Ibadan
(1991 - 1993) MBA (mul) Fassara
Thesis director Adebayo Dada Akinde (en) Fassara
Dalibin daktanci Bamidele Ayodeji Oluwade (en) Fassara
Babatunde Opeoluwa Akinkunmi (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da university teacher (en) Fassara
Employers Jami'ar Ibadan

Adenike Osofisan (An haife ta ranar 11 ga watan Maris, 1950). Ta kasance farfesar kimiyyar na’ura mai kwakwalwa ce wacce ta gwanance ta kware a fannin tattara bayanai da kuma kula da ilimi. Ita ce mace ta farko ‘yar Nijeriya da ta fara samun ilimi mai zurfi har zuwa matakin digirin digirgir (PhD) a fannin kimiyyar kwamfuta, wacce ta fara taka wannan damar tun a 1989. A shekarar 2006, ta zama cikakkiyar Farfesa a jami’ar Ibadan, hakan ya kai ta ga zama mace ta farko a dukkanin nahiyar Afrika da ta fara zama Farfesar kimiyyar kwamfuta.[1]

Tarihin Rayuwa da Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

Adenike Osofisan ta kammala karatun sakandarinta ne a Fiwasaiye Girls’ Grammar School, da ke Akure, da kuma Comprehensice High School, Ayetoro a 1968. A tsakanin 1971 da 1976, ta samu digirinta na farko a jami’ar Ile-Ife, ta samu tallafin karatu daga gwamnatin tarayya tun a wancan lokacin bisa kokarinta inda ta kammala jami’a cikin cin moriyar wannan tallafin. Daga baya ta zo ta wuce zuwa cibiyar ilmin kimiyya ta Georgia a 1978, ta samu digirinta na biyu ne a Information and Computer Science a shekarar 1979. Ta kuma yi digirinta na uku (PhD) kan darasin ‘Data Processing Model for a Multi-access Computer Communication Network’ wacce ta kammala a 1989 a jami’ar Obafemi Awolowo a karkashin sanya idon Adebayo Akinde. A 1993, ne ta kammala wani shiri na musamman a fannin iya gudanar da harkokin kasuwanci da ririta kudade a jami’ar Ibadan.[2]

Farfesa Osifisan ta fara aikin koyarwa ne a kwalejin kimiyya ta Ibadan a shekarar 1979. Ta kwashe tsawon shekaru tana koyarwa a wannan kwalejin daga baya har ta zo ta zama shugabar tsangayar kimiyya na wannan kwalejin. A 1999 ne kuma ta fara aiki da jami’ar Ibadan, nan take ta fara aiki a matsayin mai rikon mukamin shugaban sashin kimiyya na jami’ar. A 2003, ta samu likafarta ya daukaka zuwa karamar farfesa, kama-kama ta samu zuwa ga matakin cikakkiyar Farfesa ne a shekarar 2006. Har-ila-yau, ta kasance malamar jami’ar da ke koyarwa na wucin gadi a jami’ar Legas.[3]

Adenike Osofisan ta kasance mambar majalisar amintattu na Nigeria Internet Registration Association (NIRA); tsohowar mambar cibiyar ilimin lissafi ta kasa ‘Nigeria Mathematical Centre’ da Nigeria Institute of Management (NIM) Councils. Yanzu haka ita mambar majalisar ilimi ce; mambar Africa Academic Board of SAP (Systems, Applications, and Products in Data Processing). Sannan kuma, Adenike ita ce Darakta a makarantar nazarin ilimin kasuwanci ta ‘Ibadan School of Business’ (UISB). Ita ce mace ta farko da aka fara zama shugabar Nigeria Computer Society College of Fellows a watan Yulin 2017.[4]

Ta amshi lambobin yabo da na shaida da dama a rayuwarta. Ta kuma yi wallafe-wallafe na littafai da mukalolin da a yanzu haka ake amfani da su a cibiyoyin ilimi da daman gaske.[5]