Akushi
Appearance
Akushi wani mazubin abinci ne wanda ake amfani da shi wajen zuba abinci dafaffe. Musamman a zamanin da, wanda yanzu kusan an daina amfani da shi saboda zuwan tekanolojin zamani nayin kayayyakin zuba abinci kala-kala, amma har yanzu idan kaje wasu ƙauyuka musamman a arewacin Najeriya suna amfani da shi Akushi. Shi dai Akushi masu yin sana'ar sassaƙa sune suke sassaƙa shi daga bishiya.
A takaice Akushi sassaƙaƙƙen mazubin abinci ne wanda ake amfani da shi kafin zuwan kwanon zuba abinci a ƙasar Hausa wani lokacin ma har da cokali ake sassaƙawa.[1][2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Akushi". rumbunilimi.com.ng. Archived from the original on 15 June 2021. Retrieved 15 September 2021.
- ↑ Musa, Aisha (17 March 2017). "Kayayyakin Amaren Hausawa guda 5 a shekarun baya". legit.hausa.ng. Retrieved 15 September 2021.