Akwasi Afrifa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
AkwasiAfrifa.png
Lt.Gen. Akwasi Afrifa

Laftanar Janar Akwasi Amankwaa Afrifa (an haife shi a 24 Afrilun shekarata 1936 - ya rasu a 26 Yunin shekarar 1979) soja ne na Ghana, manomi, basaraken gargajiya, marubuci kuma ɗan siyasa . Ya kasance shugaban kasar Ghana na mulkin soja a shekarar 1969. Daga nan ya ci gaba a matsayin manomi kuma ɗan gwagwarmayar siyasa. An zabe shi dan majalisa a 1979, amma an kashe shi kafin ya hau kujerarsa. An kashe shi tare da wasu tsoffin shugabannin kasa biyu, Janar Kutu Acheampong da Janar Fred Akuffo, da wasu Janar-Janar biyar (Utuka, Felli, Boakye, Robert Kotei da Amedume), a watan Yunin 1979.

Ilimi da Horon Aikin Soja[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan karatunsa na sakandare a kwalejin Adisadel, ya shiga aikin sojan Ghana a shekarar 1957 kuma aka tura shi zuwa Makarantar Horar da Jami'ai na Musamman. Daga nan ne ya halarci Makarantar ' Mons Officer Cadet School', Aldershot, Ingila a 1958. Sannan ya kammala karatun jami'a a Royal Military Academy, Sandhurst, England . A cikin 1961, ya kasance a Makarantar Sojan Ruwa, Hythe, United Kingdom .

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Harkar Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Afrifa ɗa ne ga Opanin Kwaku Amankwa da Ama Serwaa Amaniampong, dukkansu daga Krobo, kusa da Mampong, a Yankin Ashanti. A lokacin da aka kashe shi, ya auri Christine Afrifa, wacce ta haifa masa yara tara. Na farko Ama Serwa Afrifa, bakwai tare da Christine Afrifa; Baffour Afrifa, Baffour Anokye Afrifa, Maame Drowaa Afrifa, Serwaa Amaniampong Afrifa, Ayowa Afrifa, Sophia Afrifa da Akosua Afrifa. An haifi ɗansa na ƙarshe Henry Afrifa bayan mutuwarsa.

Littattafai[gyara sashe | gyara masomin]

 •  Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. ^ a b c d
 2. ^ a b c
 3. ^ a b
 4. ^
 5. ^ a b c d
 6. ^
 7. ^
 8. ^ a b
 9. ^
 10. ^
 11. ^
 12. ^
 13. ^
 14. ^
 15. ^
 16. ^
 17. ^
 18. ^
 19. ^
 20. ^ a b

Bayani[gyara sashe | gyara masomin]