Al-Baqir
Appearance
|
| |||
712 - 733 ← Ali ibn Husayn - Jafar as-Sadiq → | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Madinah, 8 Mayu 677 | ||
| ƙasa | Khalifancin Umayyawa | ||
| Harshen uwa | Larabci | ||
| Mutuwa | Madinah, 26 ga Janairu, 733 | ||
| Makwanci | Al-Baqi' | ||
| Yanayin mutuwa | (dafi) | ||
| Killed by |
Hisham ibn Abd al-Malik (en) | ||
| Ƴan uwa | |||
| Mahaifi | Ali ibn Husayn | ||
| Mahaifiya | Fatimah bint al-Hasan | ||
| Abokiyar zama |
Umm Farwa bint al-Qasim (en) | ||
| Yara |
view
| ||
| Ahali |
Zayd ibn Ali (en) | ||
| Ƴan uwa |
view
| ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Larabci | ||
| Malamai | Ali ibn Husayn | ||
| Ɗalibai | |||
| Sana'a | |||
| Sana'a |
Liman da muhaddith (en) | ||
| Imani | |||
| Addini | Ƴan Sha Biyu | ||



Muhammad bn Ali ( larabci : محمد بن علي الباقر), wanda aka fi sani da al-Baqir ( wanda ya bude ilimi ) (677-733) shi ne limami na biyar daga cikin limaman shia. [1] Shi ne dan Ali bin Husayn ko Zayn al-Abidin kuma imam na farko wanda ya fito daga jikokin Muhammad da Hasan bn Ali da Husayn bn Ali . Musulmin Sunni da Shia suna matukar girmama shi saboda shugabancinsa, iliminsa da kuma ilimin addinin Musulunci a matsayin masanin shari'a a Madina . Bayan wafatin Ali bn Husayn (Imami na huxu), mafi yawan ‘yan Shi’ar sun yarda da dansa al-Baqir a matsayin imami na gaba; wasu daga cikinsu suka ce, wani dan imam Zayd bn Ali shi ne imami na gaba, kuma ya zama ana kiran sa da Zaidiyyah . [2]