Jump to content

Al-Hajib Al-Mansur, Gwarzon Aldalus (Littafi)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Al-Hajib Al-Mansur, Gwarzon Aldalus (A larabce: الحاجب المنصور: أسطورة الأندلس) ne wanda shahararran marubuci dan kasar Qatar, Ali bin Ghanim Al-hajiri, ya wallafa. Ya wallafa littafin ne akan rayuwar babban gwarzo kuma shugaba mai karfin mulki Abu Amir Muhammad bin Amir wanda aka fi sani da Alhajibul Mansur. Alhajibul Mansur yayi mulki ne a kasar Andalus dake yankin kasar Ipaniya daga shekara ta 371 zuwa 392 (Hijriya) lokacin da larabawa suka mulki yankin.

Mawallafin littafi masanine akan tarihin siyasar duniya musamman yankin Asiya da Turai. Yana da littafai masu yawa da harshen Larabci wanda suka hada da "Kasar Qatar a idon matafiya" wanda aka fassara zuwa harsuna daban-daban da suka hada da Hausa da Sipaniyanci da Sinanci a shekarun baylittafi a. Ya kuma wallafa liitafi mai suna "Gwazon Malamin Afirka: Usmanu dan Fodiyo" a cikin shekara ta 2022. Sauran littafansa sun hada da "Assin fi Uyunir Rahalah" (Kasar Sin a Idon matafiya) da "Assaltanah Al-Jabriyya" da sauranzu.[1]

Kunshiya[gyara sashe | gyara masomin]

Littafin Al-Hajib Al-Mansur, Gwarzon Aldalus ya kunshe sashe guda 7:[2]

Sashe na farko: Rayuwar Al-hajibul Mansur da siffofinsa

sashe na biyu: Ababe da suka taimake Al-hajib Al-Mansur wajen samun mulki

Sashe na uku: Gwagwarmayar da Al-hajib Al-Mansur yayi wajen dakile rikice-rikice da barna

sashe na hudu: Alaka da ke tsakanin Al-hajib Al-Mansur da sauran sarakunan yankin Sipaniya da kasashen gabashin Afirka da kuma Daular Fatimiyya

Sashe na biyar: Kokarin da Al-hajib Al-Mansur yayi wajen tsara dakarun soji

Sashe na shida: Rawar da Al-hajib Al-Mansur ya taka wajen kawo ci gaba da wayewa da kuma bangaren ilimi

Sashe na bakwai: Cigaban da Al-hajib Al-Mansur ya kawo ta bangaren tsarin gine-gine a zamanin sa.

Karbuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan fitowanshi, wannan littafi mai suna "Al-hajib Al-Mansur: Gwarzon Aldalus" ya samu karbuwa ta hanya zagaye kafafin yada ilimin tarihi. Hakan ya farune saboda kasancewar ba a samu littafi guda da ya shafe bangarori daban-daban na rayuwar wannan shugaba da kuma mulkinsa ba kamar wannan. Sannan ya kuma samun karbuwa kasancewar littafin na nuna cewa duniyar larabawa da musulunci basu manta tarihi da kuma cigaba da suka kawo a yankin kasar Turai a tun a zamanin da Turai ke cikin duhu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]