Jump to content

Gwarzon Malamin Afirka: Usman Dan Fodiyo (Littafi)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Gwarzon Malamin Afirka Usman Dan Fodiyo (A larabce: أسطورة إفريقيا وعالمها الشيخ عثمان بن فودي) littafi ne wanda babban mai bincike kuma marubuci dan kasar Katar Ali Bin Ghanim Alhajri ya wallafa kan tarihin rayuwar Shehin malami Usman Dan Fodiyo a shekara 2022. Littafin ya samu karbuwa inda ya haska rayuwar malamin tun daga farkon rayuwar sa zuwa kafa sabuwar daular musulunci a Arewacin Najeriya da ma wasu yankunan gabashin Afirka. Littafin na iya kasancewa babban aikin bincike da wani balarabe yayi akan rayuwar Shehu Usman Dan Fodiyo a cikin kwanakin nan.[1][2]

Kunshiya[gyara sashe | gyara masomin]

Littafin na dauke da fasali guda hudu:

  1. Rayuwar Shehu Usman Dan Fodiyo da siffofinsa: wannan fasali ya kunshi sunansa da asalinsa da bayani kan mahaifar sa da 'ya'yansa da iyalansa har zuwa tarihin mutuwarsa. Sannan ya kuma kunshi rayuwar addininsa da irin akidunsa. Hakazalika fasalin ya kunshi ra'ayoyin shehu da kuma maganganun wasu malamai akan shi.
  2. Harkar Shehu Usman Dan Fodiyo na kawo gyara: wannan babin ya kunshi bayanai kan kira da shehu Dan Fodiyo yayi na kawo gyara a Akidu da kuma zamantakewa, yadda yayi bayani kan kulawa da ilimin da yayi, da kuma irin sanayyar da malamin yayi wa rayuwar mutanen arewa a zamaninsa. ya kuma kunshi tafiye-tafiye da malamin yayi zuwa kasar Kebbi da zamfara kasar zuma. sannan ya yi bayani akan rikice-rikice da malamin yayi da wasu daga cikin sarakunan kasan hausa kamar sarkin Gobir da su Yunfa. Sannan fasalin yayi bayani akan nasarar da Shehu Usman Dan Fodiyo ya samu wajen kafa daular musulunci a wasu yankunan Arewa kamar:

3. Kokarin Usman Dan Fodiyo wajen karfafa tsarin mulki: wannan fasalin yana dauke da tsarin mulki wannan Usman Dan Fodiyo ya kafa, ta yadda littafin ya bayyana makan iko a daular musulunci da irin rabe-rabe na yankunan daular.

4. Kokarin Usman Dan Fodiyo a fegen ilimi: a wannan fasali, marubucin littafin ya anbaci irin ci gaba da harkar ilimi ta samu zamanin Usman Dan Fodiyo. Ya kuma ambaci iri gudunmawar da malamin ya bayar wajen karatun mata a wannan zamin. Fasalin ya tabo gefen gudunmawar malamin wajen rubuce-rubucen littafai da wake irin na labaci.[3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://islamonline.net/%D9%83%D8%AA%D8%A7%D8%A8-%D8%A5%D9%81%D8%B1%D9%8A%D9%82%D9%8A%D8%A7-%D8%B9%D8%AB%D9%85%D8%A7%D9%86-%D9%81%D9%88%D8%AF%D9%8A/
  2. Ali Bin Ghanim Alhajri: أسطورة إفريقيا وعالمها الشيخ عثمان بن فودي, Difaf: 2022
  3. https://www.alukah.net/culture/0/154290/%D8%A5%D8%A8%D8%B1%D8%A7%D8%B2-%D8%AC%D9%87%D9%88%D8%AF-%D8%A7%D9%84%D8%B4%D9%8A%D8%AE-%D8%B9%D8%AB%D9%85%D8%A7%D9%86-%D8%A8%D9%86-%D9%81%D9%88%D8%AF%D9%8A-%D8%A7%D9%84%D8%B9%D9%84%D9%85%D9%8A%D8%A9-%D9%85%D9%86-%D8%AE%D9%84%D8%A7%D9%84-%D9%83%D8%AA%D8%A7%D8%A8-%22%D8%A3%D8%B3%D8%B7%D9%88%D8%B1%D8%A9-%D8%A5%D9%81%D8%B1%D9%8A%D9%82%D9%8A%D8%A7-%D9%88%D8%B9%D8%A7%D9%84%D9%85%D9%87%D8%A7-%D8%A7%D9%84%D8%B4%D9%8A%D8%AE-%D8%B9%D8%AB%D9%85%D8%A7%D9%86-%D8%A8%D9%86-%D9%81%D9%88%D8%AF%D9%8A%22-%D9%84%D9%84%D8%AF%D9%83%D8%AA%D9%88%D8%B1-%D8%B9%D9%84%D9%8A-%D8%A8%D9%86-%D8%BA%D8%A7%D9%86%D9%85-%D8%A7%D9%84%D9%87%D8%A7%D8%AC%D8%B1%D9%8A/